Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare, ya rattaɓa hannu kan wata doka da za ta zaftare yawan ma’aikatun gwamnatin jihar daga 28 zuwa 16.
Gwamnan ya ɗauki wannan matakin ne domin dakatar da almubazzaranci a cikin gwamnati tare da kawar ma’aikatun da ke maimaita ayyuka.
Wannan bayanin ya fito ne a wata sanarwa a ranar Alhamis ta hannun mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris.
Ya ce gwamnan ya rattaɓa hannu a kan dokar ne a ranar Alhamis a zauren majalisa da ke gidan gwamnati a Gusau.
Sabbin ma’aikatun da aka amince da su sune na noma; kasafin kuɗi da tsare-tsare; Kimiyya da Fasaha; Muhalli da Albarkatun ƙasa; Kuɗi; Lafiya; da Kasuwanci; cinikayya da Masana’antu.
Gwamnatin tarayya za ta magance ambaliyar ruwa a Jigawa – Shettima
Sauran su ne Labarai da Al’adu; shari’a; gidaje da ci gaban Birane; al’amuran ƙananan hukumomi da masarautu; Al’amuran Addini; Harkokin Mata da ci gaban al’umma; Ayyuka da walwala; Matasa da Wasanni; Tsaron Cikin Gida da Harkokin Cikin Gida.
Sannan har wala yau, gwamnatin jihar ta biya cikakken albashin ma’aikata da ta gada, ciki har da na watan Yunin da ya gabata.