No menu items!

Sample Page Title

Date:

Rahotanni sun nuna akwai yiwuwar ɗan wasan gaba na Real Madrid Karim Benzema na shirin komawa ƙasar Saudi Arabiya da taka leda bayan ƙarewar kwantiraginsa da ƙungiyar.

Sashen labaran wasanni na ESPN ya bayyana cewa Saudi Arabiya ta yi wa Benzema tayin kwantiragin shekaru biyu kan farashin yuro miliyan 400 don komawa can ƙasar da taka leda a watan Janairu, wanda zai bashi damar haɗewa da Cristiano Ronaldo na Portugal da ya koma Al Nassr da taka leda bayan raba gari da Manchester United a ƙarshen waccan kakar.

Benzema ɗan Faransa mai shekaru 35 da ya lashe kyautar Ballon d’Or a shekarar 2022 wasu bayanai sun nuna cewa ɗan wasan ya cimma yarjejeniya da Madrid don tsawaita kwantiraginsa zuwa ƙarin shekara guda a nan gaba.

Madrid dai ta gamu da mummunar kaka a wannan karon bayan rasa kofunan La Liga dana zakarun Turai sakamakon mummunan shan kaye hannun Manchester City a wasan gab da na ƙarshe ko da ya ke ta yi nasarar lashe kofin Copa Del Rey.

Baya ga Benzema Saudiya na kuma harin manyan ‘yan wasan da suka ƙunshi Lionel Messi da Sergio Busquets da Jordi Alba.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...