EFCC da Saudiyya sun cimma yarjejeniya don ƙwato kadarorin gwamnati da aka sace

1
276

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta cimma yarjejeniya da ƙasar Saudiyya don ganin an ƙara samun nasarar ƙwato kadarorin gwamnati da aka sace.

Shugaban hukumar Abdulrasheed Bawa, yayin rattaba hannu kan yarjejeniyar a birnin Jeddah da hukumar yaƙi da rashawa ta Saudiyya NAZAHA, ya ce hakan zai taimaka wajen daƙile masu aikata rashawa.

KU KUMA KARANTA: Hukumar EFCC ta kama tsofaffin masu laifi 61 bisa laifin zamba a intanet a Ilori

Abubuwa da shugaban na EFCC da tawagarsa suka tattauna a takwarorinsu na Saudiyya a ziyara da suka kai, ya haɗa da yadda za a ƙara ƙaimi wajen ƙwato kadarori da wasu ke sacewa su kai ƙasar.

Bawa ya ce za a samu nasara ne kaɗai ta hanyar tattara bayanan sirri da samun bayanai a kan lokaci daga wajen hukumomi masu yaƙi da rashawa da kuma takwarori na ƙasashen waje.

1 COMMENT

Leave a Reply