No menu items!

Sample Page Title

Date:

Wata budurwa mai shekara 20 ta kai mahaifinta ƙara kotu kan ƙoƙarin yi mata auren dole.

Matashiyar mai suna Fatima Aliyu daga garin Kaduna ta shaida wa kotun shari’ar Musulunci cewa tana da wanda take so, amma mahaifinta ke ƙoƙarin yi mata auren dole.

Mahaifin ya ce iyayensa kafin su rasu ne suka zaɓa wa ɗiyarsa mijin aure, shi ya sa yake ƙoƙarin cika alƙawari.

KU KUMA KARANTA: Cin Amana: Kotu ta raba auren da ya yi shekaru 15

Alƙali Malam Aiyeku Abdulrahman, ya ce duk da yake mahaifi na da damar zaɓawa ‘yarsa mijin aure, a wannan gaɓar ƙoƙarin tilasta mata bai dace ba.

Ya shawarci mahaifin ya ƙara haƙuri da ɗiyar tasa.

Alƙalin ya buƙaci mahaifin ya bai wa ‘yarsa damar gabatar da mutumin da take so, sannan a yi bincike, idan babu wani laifi to a bar su su yi aurensu.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

1 COMMENT

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...