Cin Amana: Kotu ta raba auren da ya yi shekaru 15

2
451
Ta kama mijinta yana lalata da ’ya’yan cikinsu

Wata Kotu a Upper Area dake Gwagwalada, Abuja, ta raba mata da miji waɗanda suka yi shekaru 15 da aure, wato wani ma’aikacin gwamnati, Okpanachi Yahaya da matarsa, Zainab Adejoh bisa zargin cin amana.

Alƙalin kotun, Abdullahi Abdulkareem ne ya raba auren kamar yadda shari’ar Musulunci ta tanada, bayan da Yahaya ya nemi sakin bisa dalilan cin amana.

Abdulkareem ya umurci Adejoh da ta yi “Iddah” (jiran wa’adi na shari’a) na wata uku kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, kafin ta sake yin wani aure.

KU KUMA KARANTA: An gurfanar da wasu ma’aikatan gida biyu a kotu bisa zargin sata

Ya ƙara da cewa batun kula da yara da mai shigar da ƙara ya gabatar a gaban kotu ya kamata a shigar da shi a matsayin wata ƙara ta daban.

Tun da farko dai wanda ya shigar da ƙarar ya shaidawa kotun cewa ya auri wanda ake ƙara bisa shari’ar Musulunci a ranar 14 ga Satumba, 2009 kuma ya albarkace shi da ‘ya’ya biyu masu shekaru 14 da 12.

Ya ce ya lura cewa wanda ake ƙara ta fara cin amanarsa a shekarar 2019.

“Na ga Adejoh tana ɓoya a cikin kicin tana waya da wani mutum, kuma da na yi mata tambayoyi, sai ta yi min faɗa har da duka ,” in ji Yahaya.

Ya ce ya yi rashin lafiya a cikin watanni huɗu da suka gabata, an kwantar da shi a Asibiti, daga bisani aka kai shi ƙauyensu da ke Kogi amma wanda ake ƙara ba ta taɓa ziyarce shi ba kuma ta ci gaba da mu’amalarta.

Ya ce wanda ake ƙara ta je ofishinsa ne a lokacin da yake can ƙauyen ta karɓi kuɗi a madadinsa ba tare da izininsa ba.

Yahaya ya ce an gano ne bisa ƙa’idarsa da kuma al’adar sa cewa tushen ciwon nasa shi ne haramtacciyar alaƙa da wanda ake ƙara da wasu mazan.

“’Yan uwana ne suka gayyace Adejoh domin sasanta rikicinmu amma ta ƙi.

“Babu sauran soyayya da zaman lafiya a cikin auren,  Ina son a raba auren,” in ji shi. Wanda ake ƙara, duk da haka, ta amince da sakin.

2 COMMENTS

Leave a Reply