Gwamna Zulum ya tura marayu 19 koyon karatun likita a Masar

A ranar Laraba ne Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya sallami matasa 19 waɗanda akasarinsu sun taso ne a matsayin marayu da marasa galihu a jihar Borno, a lokacin da suke kan hanyarsu na zuwa ƙasar Masar domin yin karatun likita

Ɗaliban sun tashi zuwa birnin Suez na ƙasar Masar don yin karatu da samun digiri na farko a fannin likitanci da tiyata (MBBS) kan cikakken tallafin karatu na gwamnatiin jihar na tsawon shekaru biyar.

Tallafin karatu na Jami’ar Suez wanda Zulum ya bada kuɗi naira miliyan 250, kaɗan ne daga cikin cigaban da aka samu sakamakon ziyarar da Gwamna Zulum ya kai wasu Jami’o’in kasar Masar a watan Nuwamban 2020.

Gwamnan ya yi alƙawarin amincewa da tallafin karatu ga matasa daga cikin ‘yan uwa da suka fi fama da talauci a Jihar Borno, domin su yi karatu a Masar, da sauran ƙasashen da kuma fadin Najeriya.

Zulum, daga baya a watan Fabrairun 2022, ya kai ziyarar bi-da-bi a ofishin jakadancin Masar da ke Abuja domin ganawa da Ambasada Ihab Awad, domin tattaunawa kan hadin gwiwar ilimi. Matasa 19 da suka ci gajiyar wannan hadin gwiwa an zaɓo su ne daga ƙananan hukumomin Borno 27, waɗanda suka haɗa da samari 12 da ‘yan mata bakwai.

Gwamna Zulum ya karɓi baƙuncin waɗanda suka amfana 19 a gidan gwamnati dake Maiduguri.

Kwamishinan ilimi mai zurfi, kimiyya, fasaha da ƙirkire-ƙirƙire, Dakta Babagana Mustapha Mallambe ne ya jagorance su, wanda ma’aikatarsa ​​ke kula da hukumar ba da tallafin karatu ta jihar Borno.

Zulum ya taya matasan murna, sannan ya buƙace su da su maida hankali kan karatunsu, su kasance jakadu nagari na jihar Borno da Najeriya baki ɗaya.


Comments

2 responses to “Gwamna Zulum ya tura marayu 19 koyon karatun likita a Masar”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Gwamna Zulum ya tura marayu 19 koyon karatun likita a Masar […]

  2. […] KU KUMA KARANTA: Gwamna Zulum ya tura marayu 19 koyon karatun likita a Masar […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *