Daga hawansa gwamna Adeleke ya tsige sarakuna 3, ya kori ma’aikata 12,000

1
291

Gwamnan jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke ya kori ma’aikata 12,000 tare da bayar da umarnin tsige wasu sarakuna uku, ya kuma soke naɗin manyan sakatarorin dindindin guda 30 tare da daƙatar da shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Osun (OSIEC)da kuma mambobin hukumar.

Tsohon gwamnan jihar Adegboyega Oyetola ne ya ɗauki korarrun ma’aikatan da sakatarorin dindindin 30 aiki a karshen watan Yuli.

Sarakunan da Adeleke ya tsige sun haɗa da Akinrun na Ikinrun Oba Yinusa Akadiri; Aree na Ire Oba Ademola Oluponle da Owa na Igbajo, Oba Gboyega Famodun.

Gwamnan ya umarci sarakunan su bar fadar, inda ya nemi jami’an tsaro su karbe karɓe ragamar fadar, Adeleke ya kuma soke naɗin manyan sakatarorin dindindin guda 30 tare da dakatar da shugaban OSIEC da kuma mambobin hukumar OSIEC.

Tsohon gwamna Adegboyega Oyetola ya ɗauki korarrun ma’aikatan da sakatarorin dindindin 30 aiki a karshen watan Yuli.

A cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan, Olawale Rasheed ya fitar, ya ce gwamnan ya sanya hannu kan umarnin zartarwa da suka shafi batutuwan sarauta, batutuwan naɗe-naɗe, kafa kwamitin bita, tantance ma’aikata da kuma batutuwan ɗaukar aiki.

“Dukkan ayyukan da gwamnatin jihar Osun ta yi a kowane matsayi a cikin ma’aikatu da hukumomi da kwamitoci bayan 17 ga Yuli, 2022 za a soke su.

“Dokar zartarwa ta biyar akan harkokin masarautu da naɗin sarakunan gargajiya, dukkanin naɗe-naɗen sarakunan gargajiya da gwamnatin jihar Osun ta yi bayan ranar 17 ga Yuli, 2022, an ba da umarnin sake duba su don tabbatar da bin ka’idojin da suka dace na ayyana sarauta da kuma dokokin kasa, al’ada da al’adun da suka shafi irin wadannan masarautun.

“Batun Ikirun, Iree da Igbajo, don gujewa tabɓarɓarewar doka da oda, an dage nadin na Akinrun na Ikinrun, Aree na Ire da Owa na Igbajo har sai an sake nazari.

” Bayan haka, fadar Akinrun na Ikirun, Aree na Iree da Owa na Igbajo su kasance babu kowa a ciki, yayin da aka umarci jami’an tsaro da su dauki nauyin ragamarsu”

Sakataren gwamnatin jihar Osun, Tesleem Igbalaye, a wata sanarwa da ya fitar ya kuma sanar da dakatar da shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Osun Mista Segun Oladitan da mambobin hukumar, sauran sun haɗa da Yusuf Oyeniran, Suibat Adubi, Prince Yinka Ajiboye, Abosede Omibeku, Dosu Gidigbi, da Wahab Adewoyin.

1 COMMENT

Leave a Reply