No menu items!

Sample Page Title

Date:

Daga; MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI.

GWAMNAN Jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambiwal, ya bayyana cewa lokaci ya yi da Jam’iyyar PDP za ta tsayar da dan takarar shugaban kasa daga Arewacin Najeriya.

Aminu Waziri Tambuwal ya bayar da cikakken lissafin da ya tabbatar da cewa ya dace PDP ta natsu ta tabbatar da yin tariyar lissafin baya wajen yin lissafin irin mutanen da suka yi shugabancin Najeriya a tsawon shekaru 34 na mulkin Dimokuradiyya, za a ga cewa mutanen Kudancin kasar nan sun tserewa na yankin Arewa da shekaru a kalla hudu.

Ga dai lissafin lokutan da kowa ne yanki ya yi ya na Jan ragamar mulkin Najeriya ” zamanin Olusegun Obasanjo, ya yi shekaru Takwas sai kuma Goodluck Ebele Jonathan da ya yi shugabancin Najeriya na tsawon shekaru Shida, shi kuma marigayi Alhaji Umaru Musa Yar’aduwa ya yi shekaru biyu ne sai mulkin ya koma hannun Jonathan, saboda haka idan an yi lissafi za a ga cewa yankin kudu ya tserewa yankin Arewa da shekaru hudu kenan ya na gudanar da mulki a Najeriya don haka lokaci ne da PDP za ta yi karatun ta natsu ta tabbatar da tsayar da dan takarar shugaban kasa daga Arewacin Najeriya”, inji Gwamna Tambuwal.

admin
adminhttps://neptuneprimehausa.com
Ni ɗan jarida ne mai zaman kansa. Mawallafi kuma mai sharhi a lamarin yau da kullum.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...