Dattijo Ya Yi Allah-Wadai Da Hare-Haren ‘Yan Ta’adda A Kaduna

0
344

…Ya Dakatar Da Shirin Tuntuba Tare Da Bayar Da Tallafi Ga Wadanda Abin Ya Shafa

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

DAYA daga cikin jiga-jigan ‘yan takarar Gwamna a Jam’iyyar APC a Jihar Kaduna, Muhammad Sani Abdullahi (Dattijo), ya bayyana bakin cikinsa bisa ga samun labari mai ban tausayi na harin Jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna, kana da sauran hare-haren yan ta’adda da aka kai a garin Kaura, Jema’a da Giwa da ya yi sanadiyar rasa rayuka a yan kwanakin nan.

A wata sanarwa da ya raba wa manema labarai kuma mai dauke da sa hannunsa da kansa, Dattijo ya yi Allah-Wadai da hare-haren tare da jajantawa wadanda harin ya rutsa da su da iyalansu kan harin da aka kai.

Sanarwar ta ruwaito Dattijo yana cewa; “Na yi matukar bakin ciki da harin jirgin kasa da ‘yan ta’adda suka kai a ranar litinin da yammah. Tunanina da addu’o’i suna tare da wadanda abin ya shafa da kuma iyalansu kan abin bakin ciki na lamarin daya faru”.

Dattijo ya kuma jajanta wa Gwamna Nasir Ahmad El-Rufai, iyalai da masoyan wadanda harin jirgin kasan Kaduna, Kaura/Jema’a da Giwa ya rutsa da su tare da addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu sakamakon harin, da yin addu’ar samun lafiya ga wadanda suka jikkata.

“Ina mika ta’aziyyata ga babanmu kuma shugabanmu, Malam Nasir El-Rufai, iyalai da wadanda harin ya shafa.” Dattijo ya ce.

Dattijo ya kuma yabawa jami’an tsaro bisa ga kokarin da suka yi na kai dauki da irin kwarewarsu, sannan ya bukace su da su karfafa aikin hadin gwiwa domin tabbatar da samun nasara a bisa tsarin da Gwamnatin El-Rufai ta yi a fannin tsaro.

“Aikin hadin gwiwa domin ayyukan ceto abin yabawa ne amma ina kira da a samar da hadin kai tsakanin Jami’an tsaro domin samun nasarori a tsarin hada hannu da karfe da gwamnatin Jihar Kaduna ke shiryawa a fannin tsaro domin dakile duk wasu ayyukan ta’addanci a Jihar,” in ji Dattijo.

“A halin da ake ciki, an dakatar da duk wasu ayyuka Kamfen dina da aka shirya a ci gaba da rangadin karamar hukumar da tuntuba na neman tsayawa takara har sai wani lokaci.”

Sanarwar ta kuma sanar da bayar da gudummawar da ba a bayyana adadinsu ba ga wadanda harin ya rutsa da su.

Leave a Reply