Za Mu Ci Gaba Da Bunkasa Harkar Noma A Najeriya – CBN

0
320

Daga; MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI.

AN bayyana Babban Bankin Najeriya, (CBN) a matsayin wanda zai kara bunkasa harkokin Noma da ci gaban kasa baki daya.

Da yake zantawa da manema labarai, Wakilin babban Bankin Najeriya Mista Philip Yila Yusif, ne ya bayyana hakan
a wajen babban taron kaddamar da Dalar Masarar da aka karba a hannun manoman da Bankin ya ba rancen yin Noma da aka yi a Kaduna.

Philip Yila Yusif, wanda ya wakilci Gwamnan babban Bankin Najeriya Godwin Emefele, a wajen kaddamar da Dalar Masara karo na biyu da aka yi ta hanyar hadin Gwiwa tsakanin babban Bankin Najeriya da kungiyar masu kokarin Farfado da Noman Masara ta MAAN, ya ce daya daga cikin dalilan da ya sa ake yin wannan Dalar Masara shi ne domin a tabbatarwa da Jama’a cewa babban Bankin kasa zata iya jagoranci wajen dawowa da irin Dalar kayan amfanin Gona da aka Sani a can baya

“Mun yi Dalar Shinkafa kuma yau ga shi an yi Dalar Masara wanda ke nuni da cewa hakika Manoman Masara na kokari wajen yin Noma ta hanyar yin amfani da kayan Noman da suke karba daga babban Bankin Najeriya bisa tsarin saboda haka wannan abin farin ciki ne kwarai.

“Kuma dukkan wannan Masarar da muka tara za mu Sayarwa masu masana’antun yin abincin Kaji da kamfanonin da ke sarrafa Masara domin amfanin al’umma ta yadda za a samu saukin farashi a kasuwa, kuma a bisa binciken da muke yi ana samun saukin farashi kwarai a Kasuwannin sayar da amfanin Gona, musamman ga masu yin abincin Kaji sun tabbatar da samun sauki kwarai.

Ya kuma bayyana kungiyar masu kokarin samar da Masara ta kasa a matsayin muhimman mutanen da babban Bankin Najeriya ke alfahari da su wajen kokarin biyan abin da aka ba su da kayan Noman da suka Noma, domin mu na yin aiki tare da su a tsawon shekaru biyar da suka gabata.

Don haka zan iya gaya maka cewa su na biyan abin da aka ba su, sai kuma akwai wadansu kamfanonin Noma da suma suke kokari irin kamfanin “AFEX” ko a Daminar Bara da ta gabata sun biya kashi dari bisa dari na abin da aka ba su a daminar Bara.

“Zan yi amfani da abin da Gwamnan Babban Bankin Najeriya ya ce ba ma son tsabar kudi, mu na son kayan amfanin Gonar da aka Noma ne kawai. Kuma muna ajiye shi ne a wuri mai kayau da zarar an samu hauhawar farashin amfanin Gona sai babban banki ya fito da shi a sayar wanda hakan na taimakawa kwarai a samu ragowar farashin kayan amfanin Gona a duk fadin kasa baki daya.

Ana nan ana aikin Farfado da tsarin yin musaya da amfanin Gona da aka samu, kuma kafin nan da tsakiyar wannan shekarar za a ga cewa wannan bangaren da ake kokarin farfadowa da shi zai ci gaba da aiwatar da aiki kamar yadda ya dace, ta yadda za a samu biyan bukata ta hanyar kara bunkasa harkokin Noma a Najeriya.

Philips, ya ci gaba da cewa idan kamfani na bukatar ayi hulda da ita, babban Banki zata duba bukatar farko sannan da karfin kamfani shin ya kai mai samar da metric ton 120 kuma yaya tazara a kasuwa ka tu na fa babban aikin Bankin Najeriya shi ne ya dai- daita farashi ba mu son farashi ya kasa tsaya wa wuri daya don haka sai a duba aga me za a iya yi domin ba a son a ba su da yawa ya zama ya yi yawa domin ya na iya shafar kasuwa shi yasa ake kokarin tsayar da farashi wuri daya.

“Muna bayar da kudi domin samar da kayan Noma sama da guda 21, don haka muka fi Sanya muhimmanci ga wasu kwarai kamar Masara, Auduga da sauransu da nufin sama masu Darajar da ta dace, don haka manufar da ta Sanya ake samar da wannan Dalar Masara shi ne a nunawa duk duniya cewa Gwamnati na samun abin da take bayarwa ga manoma kuma a kara masu kwarin Gwiwar yin Noman.

Don haka abin da ake gani a yanzu Bankin zai dauki ragama kuma da abin da ake gani a yanzu da kuma na dimbin Masarar da ke a wuraren ajiya daban daban.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here