Zan Ci Gaba Da Inganta Rayuwar Marayu Da Mabukata – Matawallen Kazaure

0
534

Daga; MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI.

DAN takarar Gwamnan Jihar Jigawa karkashin jam’iyyar PDP Alhaji Bashir Adamu (OFR) Matawallen Kazaure, da ake yi wa lakabi da Jumbo” ya bayyana harkar taimakawa marayu da marasa galihu da ke cikin al’umma a matsayin abin da zai ba muhimmanci domin a samu ingantar harkokin rayuwa baki daya.

Alhaji Bashir Adamu, (Jumbo) ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi a wajen karbar bakuncin shugabannin kungiyar Ayan Almajiri empowerment”, karkashin jagorancin Sani Daura, da suka kai masa ziyara a gidansa da ke birnin Kano.

Alhaji Bashir, ya ci gaba da bayanin cewa yana murna kwarai matuka da samun labarin wannan Kungiyar da ke kokarin ganin rayuwar marasa galihu ta inganta sun yi kyakkyawar rayuwar da ta dace.

“Wannan aiki ne na ganin an samu al’ummar ingantacciya saboda haka aiki ne na lada wanda zai iya yi wa mutum jagorancin zuwa Aljannah a ranar gobe kiyama, don haka ina farin ciki kwarai da wannan aikin da kuke yi kuma ina fata kawai a dauke ni a cikin masu yin wannan aikin domin taimakawa marayu,Almajirai da sauran dukkan marasa galihu a cikin al’umma”.

“Dama ni buri na shi ne in kyautatawa Jama’a ta yadda rayuwar kowa za ta inganta musamman a fara daga Jihar Jigawa inda nake har na zama Matawallen Kazaure kuma na zama dan majalisa har shekaru 16 a majalisar wakilai ta kasa, na kuma yi nasarar shugabantar kwamitoci har shida kwamitin karshe shi ne na harkokin tsaro a majalisar wakilai ta kasa da ke Abuja inda ke da wakilcin Najeriya baki daya”.

Tun da farko Alhaji Sani Daura, ya bayyana cewa dalilin zuwansu shi ne domin kawo ziyarar bangirma da kuma bayyana masa irin ayyukan kungiyar.

Ya ce “muna tare domin muna son ganin mun shiga cikin wannan fafutukar ta Gwagwarmayar fadakar da Jama’a su ci gaba da bayar da cikakken hadin kai da goyon baya ga tafiyar da ake yi ta yadda kowa zai amfana idan Allah ya sa an kai ga zama Gwamnan Jihar Jigawa.”

“Mu na fatan za mu hada Gwiwa da kai da kuma wannan kungiya ta mu domin zama gatan marasa gata”.

Leave a Reply