Hada Kan Manoma Da Makiyaya:  Kungiyar AFAN Reshen Jihar Jigawa Ta Ciri Tuta

0
388


  • JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

    Babu shakka, kungiyar manoma ta kasa reshen jihar Jigawa watau (AFAN) ta ciri tuta wajen kokarin da take yi na tabbatar da cewa rikice-rikice da rashin zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya bai yi tasiri ba a fadin jihar musamman ganin yadda kungiyar take aiki dare da rana wajen dakile duk wani yunkuro na fadace-fadace tsakanin bangarorin biyu.

    Wakilin mu wanda ya sami ziyartar jihar ta Jigawa ya duba yadda kungiyar ta  AFAN a jihar bisa shugabancin Alhaji Idris Yau Mai Unguwa take aikin tabbatar da cewa dukkanin wani yunkuri na  rikicin manoma da makiyaya an dakile shi cikin nasara  da sanin ya kamata, sannan kungiyar tana bakin  kokarin ta  wajen kawo sulhu da hadin kai tsakanin bangarorin biyu.

    Haka kuma a dukkanin garuruwa da kauyuka da wakilin namu ya ziyarta, ya gano cewa rikicin manoma da makiyaya baya tasiri a jihar ta Jigawa saboda kokarin da shugabannin kungiyar ta AFAN keyi dare da rana don tabbatar da ganin ana ci gaba da zaman lafiya da kwanciyar hankali tsakanin manoman jihar da kuma makiyaya a kowane lungu da sako.

    A garin gidan Lage, yankin Karamar hukumar Ringim, wani manomi mai suna Malam Dan Larai ya shaidawa Albishir cewa ” a matsayi na na manomi a wannan yanki, ina na gamsu da yadda  shugabannin mu na AFAN bisa jagorancin Alhaji Idris Yau Mai Unguwa  suke yi wajen ganin ba’a  samun munanan rikice-rikice tsakanin mu da makiyaya ba, kuma wannan ya taimaka wajen samun zaman lafiya da hadin Kai da kuma mutunta juna a wannan yanki namu”.

    Haka kuma a  Karamar hukumar Kafin Hausa wakilin mu ya gana da wani makiyin shanu mai suna Adamu Gide inda ya bayyana cewa suna samun fadakarwa daga kungiyar manoma cewa kada su shiga guraren da amfanin gona yake. Sannan ya nunar da cewa fadan manoma da makiyaya a jihar Jigawa yayi sauki saboda kokarin da kungiyoyin su keyi na tabbatar da cewa ana zaman lafiya.

    Bugu da karai, a garin ganuwar kuka, yankin Karamar hukumar Auyo, wakilin mu ya zanta da Malam Musa Idris manomi Kuma makiyayi wanda ya bayyana cewa a matsayin sa na manomi kuma makiyayi, ya gamsu bisa yadda kungiyar AFAN reshen jihar ta Jigawa take kokarin wayar masu dakai dangane da illolin fadace-fadace tsakanin manoma da makiyaya.

    Bisa wadannan abubuwa da hujjoji da  manoma da makiyaya suka bayyana, kungiyar manoma ta AFAN reshen  jihar Jigawa ta kasance abar misali duk da cewa a baya an dan yi fadace-fadace tsakanin bangarorin biyu har an Sami asarr rayuka da dukiyoyi, amma dai kungiyar ta taka mujimmiyar rawa dangane da zaman lafiya da aka samu.

    Da yake nasa tsokacin, Shugaban kungiyar manoma ta AFAN reshen jihar Jigawa, Alhaji Idris Yau Mai Unguwa ya bayyana cewa ” babu shakka muna Kokari wajen dakile dukkanin wani abu da ya taso Wanda ya shafi rikici tsakanin manoma da makiyaya a wannan jiha ta Jigawa, sannan muna Kokari sosai wajen fadakar da manoma da su kasance masu hakuri da bin dokoki wanda hakan ya taimaka Kwarai wajen samun nasarar magance wadannan rikice-rikice da ake samu”. 

    Sannan ya nunar da cewa gwamnatin jihar Jigawa bisa jagorancin gwamna Muhammad Badaru Abubakar tana yin dukkanin abubuwan da suka kamata wajen tabbatar da cewa kowane bangare na manoma da makiyaya suna samun kulawa ta musamman, don haka muke Kara jinjinawa maigirma gwamna saboda yadda muke samun wannan kulawa a gwamnatance.

    A karshe, Idris Yau Mai Unguwa ya Yi amfani da wannan dama inda ya Yi Kira na musamman ga manoman jihar ta Jigawa da kuma makiyaya da su ci gaba da zama lafiya domin kowa youana bukatar hadin Kai daga kowane bangare a matsayin masu sana’ar noma da kiwo, sannan ya yabawa sauran mataimakan sa na matakin jiha da kananan hukumomi saboda hada hannu da aka yi ana aiki tare.
  • Reply

Leave a Reply