Ɗan Bello da Abba Hikima sun kai ƙara kotu, kan riƙe albashin matasa na N-Power

0
522
Ɗan Bello da Abba Hikima sun kai ƙara kotu, kan riƙe albashin matasa na N-Power
Ɗan Bello tare da Barista Abba Hikima a bakin Kotun

Ɗan Bello da Abba Hikima sun kai ƙara kotu, kan riƙe albashin matasa na N-Power

A ranar Alhamis, 17 ga Yuli 2025, Dakta Habib Galadanci (Ɗan Bello) da Barista Abba Hikima suka kai gwamnatin Najeriya ƙara a babbar kotun ma’aikata ta ƙasa da ke Abuja saboda ƙin biyan albashin matasan N-Power da cin zarafinsu da yi musu rashin adalci.

Ƙarar me lamba NICN/ABJ/204/20225 na ɗauke da matasa 231,871 a madadin sauran da suka yi aikin N-Power ba tare da biyansu haƙƙinsu ba.

KU KUMA KARANTA: Yadda aka kama Ɗan Bello da sake shi a filin jirgin sama na Kano

ABIN DA SUKA NEMA DAGA KOTU:

1. A biya dukkan alawus da matasa ke bin gwamnati
2. A biya su biliyan ₦5 a matsayin diyyar rauni da aka ji musu sakamakon gaza biyansu
3. A biya miliyan ₦50 kuɗin ɗawainiyar shari’a
4. A Ayyana cewa abin da gwamnati ta yi na gaza biyan waɗannan matasa bayan sun gabatar da ayyukansu, haramun ne, cin zarafi ne kuma ya saɓa wa dokar ƙasa da ƙa’idodin aikatau na duniya ne.

Waɗanda aka kai ƙara sun haɗa da:
– Ma’aikatar Harkokin Jinƙai da Rage Talauci ta Tarayya
– Akanta Janar na Ƙasa
– Attoni Janar na Ƙasa
– Mista Akindele Egbuwalo (Shugaban Shirin N-Power)

Wannan ba wai batun albashi kaɗai bane – wannan magana ce ta mutunci, gaskiya da adalci.

Wanda suka sa hannu:
Barr. Abba Hikima, E. O Ekaun, H.S. Bello Esq, Ridwan Yunusa Esq
(A.A. Hikima & Co., Kano).

Leave a Reply