Ƙungiyar ‘yan jarida ta jihar Yobe ta taya gwarazan gasar Turanci ta duniya murna
Ƙungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ), reshen jihar Yobe, ta yabawa Nafisa Aminu, Rukayya Fema, da Hadiza Kalli a matsayin zakarun gasar duniya a gasar muhawarar sadarwa ta harshen turanci ta TeenEagle na shekarar 2025.
A cikin wata sanarwa da shugaban ‘yan jarida na Yobe ya fitar, Kwamared Rajab Mohammed, ya bayyana cewa ƙungiyar ta nuna matuƙar alfahari da wannan gagarumin nasarar da ɗaliban uku ‘yan asalin jihar Yobe suka samu, inda ta bayyana nasarar da suka samu a matsayin shaida na bunƙasar ilimin matasa a jihar.

Kwamared Rajab ya yabawa ‘yan gasar uku bisa yadda suka ɗaga darajar jihar Yobe a fagen duniya, ya kuma bayyana su a matsayin misalan ƙwazon ilimi. Ya kuma yaba da rawar da gwamnatin Mai Mala Buni ke taka wa wajen samar da yanayi mai taimaka wa ci gaban matasa da bayyanar da duniya baki ɗaya.
“Nasarar da suka samu ya ƙara mana sabon fata ga makomar Yobe. Waɗannan ‘yan mata sun tabbatar da cewa idan aka samar da yanayi mai kyau, matasanmu za su iya yin fice a duniya,” in ji shi.
Ƙungiyar ta NUJ ta taya zakarun murna tare da ƙarfafawa sauran matasa ƙwarin gwiwa kan nasarar da suka samu.









