Ƙungiyar likitocin Najeriya ta yaba wa Gwamna Abba bisa gyara asibitoci 200 a Kano

0
289
Ƙungiyar likitocin Najeriya ta yaba wa Gwamna Abba bisa gyara asibitoci 200 a Kano
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf

Ƙungiyar likitocin Najeriya ta yaba wa Gwamna Abba bisa gyara asibitoci 200 a Kano

Ƙungiyar Likitoci ta Kasa (NMA), reshen jihar Kano, ta yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa gyaran sama da cibiyoyin kula da lafiya Matakin farko guda 200, tare da ɗaukaka wasu daga cikinsu da ƙananan asibitoci zuwa manyan asibitoci.

Shugaban NMA na Kano, Dakta AbdulRahman Ali, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata a Kano, yayin bikin makon likitoci na shekarar 2025.

Dakta Ali ya ce wannan ƙoƙari zai inganta tsarin kula da lafiya a jihar, tare da ƙara walwalar ma’aikatan lafiya a fadin Kano.

KU KUMA KARANTA: Gwamnan Kano ya tarbi tagwayen da aka haifa a haɗe, bayan an yi aikin raba su a Saudiyya

Ya ce matakan da gwamnati ta ɗauka za su ƙarfafa ma’aikatan lafiya su ƙara himma wajen gudanar da aikinsu.

Ya roƙi gwamnatin jihar da ta tabbatar da cewa an samar da yanayi mai kyau da albashi mai kyau ga ma’aikatan lafiya domin ƙara musu ƙwazo.

Shugaban ya kuma buƙaci gwamnati ta mai da hankali kan horar da ma’aikatan lafiya da sake horar da su don samun ingantaccen sakamako a hidimar lafiya.

Haka kuma, ya yi kira ga gwamnati da masu zaman kansu masu ruwa da tsaki a fannin lafiya da su haɗa kai domin cimma manufofin samar da ingantacciyar lafiya ga jama’a.

Dakta Ali ya tabbatar da cewa mambobin NMA za su ci gaba da goyon bayan manufofin gwamnatin jihar da ke da nufin bunƙasa harkar lafiya.

Leave a Reply