Ƙungiyar likitoci ta janye yajin aikin da ta shiga

0
337

Ƙungiyar lokitoci masu neman ƙwarewa a Najeriya ta janye yajin aikin da ta shiga bayan kwana 17, inda likitocin za su ci gaba da aiki daga yau Asabar.

Shugaban ƙungiyar National Association of Resident Doctors (NARD), Dakta Emeka Orji, ya faɗa wa BBC cewa sun jingine yajin ne bayan gwamnatin tarayya ta amince da kafa gidauniyar horaswa ta ‘Medical Residency Training Fund’.

Ya ƙara da cewa gwamnatin ta fara shirin biyan su alawus na rage wahalar aikin da suke sha a asibitocin gwamnati sakamakon ficewar likitoci zuwa ƙasashen waje, kamar yadda suka nema.

A cewar Dakta Orji, waɗannan ne manya daga cikin buƙatun nasu kuma za su zauna don duba cigaban da aka samu nan da mako biyu.

KU KUMA KARANTA: Likitocin Najeriya sun yi barazanar yajin aiki a Nasarawa

Likitocin waɗanda su ne kashi 60 cikin 100 na kafatanin likitocin gwamnati a Najeriya, sun ƙaurace wa ayyuka ranar 26 ga watan Yuli, suna masu neman ƙarin kulawa da kuma inganta yanayin aikin nasu.

Leave a Reply