Ƙasar Iceland, garin da babu sauro, babu kyankyaso

2
516

Reykjavik ne babban birnin ƙasar Iceland, ƙasar da babu sauro, babu kyankyaso. Birnin Reykjavik dake gaɓar tekun Iceland, shi ne babban birnin ƙasar kuma birni mafi girma. Birnin ya na da yawan jama’a 122,853, a lissafin shekarar 2016 a Cewar Majalisar Ɗinkin Duniya.

Mafi kyawun lokaci don ku ziyarci birnin Reykjavik, shi ne daga watan Yuni zuwa Agusta. Ba wai kawai za ku iya jin daɗin yanayin ɗumi ba (irin na Iceland, aƙalla), amma kuma za ku ji daɗin dogon kwanaki (in da ake shafe sa’o’i 21 Rana ba ta faɗi ba, al’amarin da ake yi wa laƙabi da “Rana ta tsakar Dare”). “Midnight Sun.”A na yin dare ne kawai na Awa 3, a cikin watan Yuni zuwa Agusta.

2 COMMENTS

Leave a Reply