Zargin Satar Mashin: An kashe matasa 2 a Zariya

0
69

Daga Idris Umar, Zariya

A cikin makon da ya gabata ne al’ummar garin Samaru dake ƙaramar hukumar Sabon Gari jihar Kaduna murnar su ta koma ciki.

Abin ban tausayi shi ne wayewar garin Litinin ɗin ƙarshen azumin bana da ya yi daidai 8/4/2024 aka tsinci gawarwakin wasu matasa guda biyu sanannu a garin samaru.

Matashin na farko sunansa Suleiman Usman, ɗan shekaru 25.

Sai na biyu mai suna Adamu (Faka-Faka) ɗan shekaru 30 duk a tsinci gawarsa ne a wata gona da ke kusa da garin Basawa hanyar Hunƙuyi duk a ƙaramar hukumar Sabon Gari.

Bayan iyayen yaran sun nemi yaransu sun gajine sai labari ya watsu a cikin gari cewa an kashe wasu ɓarayin mashin har an banka masu wuta a hayar Hunƙuyi.

KU KUMA KARANTA: Wani harin bam ya kashe sojojin Nijar 6

Hakan ya sa ‘yansandan yankin suka binciki inda gawar tasu take don ɗaukar matakin bincike.

Bayan ‘yansandan sun adana gawar a a ɗakin ajiye gawarwaki a Asibitin ne da kwana ɗaya sai labari ya canza kamar haka.

Iyayen Suleman da iyayen (Ado Faka-Faka) sun ce yaransu ba ɓarayi bane an kashe sune bisa rashin sani sun je ɗiban maganin sanyine.

Hakan ya sa wakilinmu ya tuntuɓi mai magana da bakin iyayen wanda aka kashe wato Malam Ubale.

Malam Ubale ya bayyanawa manema labarai cewa yaransu sam ba ɓarayin mashin bane bisa haka ne suka nemi dama ga hukumar ‘yansanda na yankin cewa su basu gawarwakin yaransu su yi masu sallah kuma suna godiya an basu ‘ya’yansu yanzu haka an yi masu jana’iza kamar yadda addinin Islama ya tanada.

Bayan haka Malam Ubale ya ce kamar yadda aka san ɗaya daga cikin wanda ake zargin mai suna Ado Faka-Faka shi yana sana’ar bayar da maganin gargajiyane wanda hakan ya sa ya haɗu da abokinsa Suleman suka je ɗiban magani cikin dare in da a can ne suka gamu da ajalinsu ta hanyar yi masu sara da Gatari na rashin mutunci da nufin ɓarayi ne su Allah ya saka masu.

Malam Ubale ya ce su yaransu ba a taɓa kama su da wani laifin sata ba don haka duk wanda ya yi masu wanna hukunci Allah zai masu sakayya. Inji shi.

Bincike ya nuna cewa ya zuwa yanzu babu wanda yasan wanda ya kashe matasan guda biyu.

Amma wata majiyar ta ce tabbas matasa sun taka sawun ɓarawo ne a wannan dajin da aka daɗe ana fakon wasu mutane masu ƙwacewa mutane babura.

Wakilinmu ya tuntuɓi mai magana da yawun hukumar ‘yansanda jihar Kaduna ASP Mansur Hasan akan lamarin amma ya ce, da yake abin ya faru ne a lokacin hutun Sallah amma za su binciki lamarin kuma za su sanar da halin da ake ciki da zarar sun sami tabbacin yadda abin yake.

Bincike ya tabbatar da cewa ba wannan bane na farko da aka kashe mutum bisa zargin satar babur ba a garin na Samaru don haka jama’ar garin suke ƙira ga hukuma da a ɗauki matakin wayar da kan jama’a don kaucewa kashe ran ɗan’dam babu wani dalili mai ƙarfi na yin kisan.

Ya zuwa yanzu babu wani mutum ko wata hukuma ko ƙungiya da ta amsa yin kisan matasan guda biyu amma dai anata Allah wadai da faruwar lamarin.

Leave a Reply