Zanga-zanga ta girgiza garuruwan Saudiyya, Iran, Masar da Lebanon saboda wulaƙanta Alkur’ani a Sweden

1
291

Gwamnatoci da dama sun gudanar zanga-zanga akan tituna a wasu ƙasashen Larabawa da ke da rinjaye a ranar Juma’a sun yi tir da sake tozarta Alƙur’ani a ƙasar Sweden.

A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Masarautar ta fitar ta ce Saudiyya, mahaifar Musulunci, ta bayyana kakkausar suka kan “makamai da ayyukan rashin ɗa’a na hukumomin Sweden” na ba da izinin “masu tsattsauran ra’ayi” su lalata kwafin Alƙur’ani.

Ma’aikatar ta ƙara da cewa za ta ƙira babban jami’in ɗan ƙasar Sweden ta miƙa masa takardar zanga-zangar.

KU KUMA KARANTA: Malaman addini a Malawi sun yi zanga-zangar nuna rashin amincewa da auren jinsi

Masar ta ce ta yi Allah-wadai da cin mutuncin Alkur’ani mai girma, tare da bayyana shi a matsayin “bayyanawa” ga ra’ayin miliyoyin musulmi a duniya.

A ƙasar Iraƙi da ke fama da taƙaddamar diflomasiyya da ƙasar Sweden, an ga masu biyayya ga fitaccen malamin Shi’a Moqtada al-Sadr suna halartar sallar Azahar a Bagadaza babban birnin ƙasar tare da wasu daga cikinsu riƙe da kwafin Alƙur’ani.

Magoya bayan Al-Sadr sun kuma gudanar da zanga-zangar nuna ɓacin rai a kudancin birnin Karbla bayan sallar Juma’a tare da ƙona tutar Sweden da ‘yan maɗigo, ‘yan luwaɗi, da maɗigo da masu canza jinsi, LGBT, kamar yadda shafin yanar gizo mai zaman kansa na Iraƙi Alsumaria News ya ruwaito.

A ƙasar Lebanon dubban magoya bayan ƙungiyar Hizbullah dake goyon bayan Iran ne suka fito kan tituna tare da gudanar da zanga zanga.

Suna ɗauke da kwafin Alƙur’ani a hannunsu, masu zanga-zangar suna rera waƙa: “Da jininmu, zamu kare Alƙur’ani mai tsarki.”

1 COMMENT

Leave a Reply