Zan yi haɗaka da sabuwar jam’iyyar ADC don a kayar da Tinubu, amma ba zan fice daga jam’iyar PDP ba – Sule Lamiɗo
Tsohon Gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamiɗo ya bayyana haka ne a hirarsa da gidan Rediyon BBC Hausa a ranar Asabar.
Lamiɗo ya ce yadda ya san halin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a kan cika burin da ya sa a gaba, na cikin abubuwan da suka ƙara masa ƙaimi wajen shiga sabuwar haɗakar jam’iyyar ‘yan hamayya ta ADC.
KU KUMA KARANTA: Jagoran PDP a Yobe, Adamu Waziri ya fice daga jam’iyar ya koma ADC
Ya ce, ya amince ya yi aiki da haɗakar ne a wani yunƙuri na kawar da gwamnatin Tinubun a babban zaɓen ƙasar mai zuwa a 2027.
Sai dai a ɓangare guda Sule Lamiɗo, ya ce ba zai fita daga jam’iyyarsa ta PDP ba, hakan wani salo ne da ke ƙoƙarin zame wa ruwan dare a siyasar Najeriyar a baya-bayan nan.
A zantawarsa da wakilinmu na Kano, Zahraddeen Lawan cikin filinmu na Gane Mini Hanya a wannan mako, tsohon gwamnan Jigawa ya fara ne da yin waiwaye kan abin da yake gani shi ne mafari na halin da siyasar Nijeriya ta samu kanta ciki.









