Za mu shiga yajin aikin sai Baba-ta-gani – ASUU

0
149
Za mu shiga yajin aikin sai Baba-ta-gani - ASUU

Za mu shiga yajin aikin sai Baba-ta-gani – ASUU

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta bayyana cewa tana shirye-shiryen shiga babban yajin aiki fiye da duk wanda aka taba yi, muddin gwamnati ta gaza aiwatar da yarjejeniyar 2009 da aka kulla tsakaninta da kungiyar.

Sashen ASUU na Jami’ar Calabar (Unical) ne ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a Calabar, ranar Talata.

KU KUMA KARANTA: ASUU ta yi fatali da sauya sunan jami’ar Maiduguri zuwa sunan Buhari

Shugaban sashen, Dr. Peter Ubi, ya ce lokaci ya yi da gwamnatin tarayya za ta cika alkawurran da suka dade suna jinkiri, wadanda aka tsara domin inganta matsayin ilimin jami’a a kasar.

Ya bayyana cewa za a fara yajin aikin da zarar babban kwamitin ASUU na kasa ya bayar da sanarwa bayan taron da za a gudanar a ranar 28 ga watan Agusta.

KU KUMA KARANTA: Ƙungiyar ASUU ta yi barazanar shiga yajin aiki a jami’ar Maitama Sule

Daga cikin bukatun da kungiyar ta jero akwai: sake duba yarjejeniyar 2009, samar da ingantaccen kudin gudanarwa ga jami’o’i, da kuma farfado da jami’o’i.

Leave a Reply