Za mu ci gaba da karya farashin shinkafa – Abdulsamad BUA
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Shugaban rukunin kamfanonin BUA, Abdul Samad Rabiu, ya yi alƙawarin kara rage farashin shinkafa da sauran kayayyakin abinci, wanda ya ce tuni ya ragu a shekarar da ta gabata.
Ya yaba wa shugaban kasa Bola Tinubu bisa yadda ya bayar da dama wajen shigo da wasu nau’ikan abinci daga waje, yana mai cewa hangen nesan shugaban ya taimaka wajen faduwar farashin kayan abinci a kasar nan.
KU KUMA KARANTA:Gwamnatin Kano da haɗin gwiwar ‘yan kasuwa sun rage farashin kayan abinci
Da yake zantawa da manema labarai a fadar gwamnatin tarayya bayan ganawarsa da Tinubu a ranar Alhamis, Rabiu ya ce kamfanin BUA ya yi amfani da damar da a ka bayar wajen shigo da nau’ikan samfarerar alkama, masara da shinkafa mai yawa.
Ya ce kungiyar manoman shinkafa sun hadar kai domin magance matsalar boye kaya da wasu kamfanoni ke yi, ya ce kungiyar ba za ta bari wani daga cikin ‘ya’yanta ya boye shinkafa ba.









