Za mu ci gaba da haɓaka Uranium a ƙasar mu — Shugaba Pezeshkian na Iran 

0
398
Za mu ci gaba da haɓaka Uranium a ƙasar mu — Shugaba Pezeshkian na Iran 
Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian

Za mu ci gaba da haɓaka Uranium a ƙasar mu — Shugaba Pezeshkian na Iran

“Ba ma son yaƙi, kuma ba za mu sakankance ba, don ba mu da tabbacin tsagaita buɗe wuta ɗin nan, (idan aka kawo mana hari) za mu kare kan mu.

Haɓaka Uranium a ƙasarmu zai ci gaba a nan gaba a cikin tsarin dokokin duniya. Ƙarfin Nukiliyar mu yana cikin tunanin masana kimiyya, ba a cikin kayan aikinmu ba.

KU KUMA KARANTA: Sayyid Khamene’i ya sake naɗa manyan Malamai 3 a majalisar tsaron Iran

Shirin nukiliyar Iran yana ci gaba da gudana, kuma duk wani ikirari na cewa wannan shirin ya dakata, ba komai ba ne illa ƙarya. Mu a shirye muke da duk wani sabon matakin yaƙin soji da Isra’ila za ta yi, kuma za mu kai farmaki har can cikinta, Sojojin mu yanzu haka na cikin shiri sosai.” Inji shi

Leave a Reply