Za a yi babban taro a kan na’ura mai ƙwaƙwalwa a Kano, ana sa ran mutane daga ƙasashe daban-daban za su halarta 

0
335
Za a yi babban taro a kan na'ura mai ƙwaƙwalwa a Kano, ana sa ran mutane daga ƙasashe daban-daban za su halarta 

Za a yi babban taro a kan na’ura mai ƙwaƙwalwa a Kano, ana sa ran mutane daga ƙasashe daban-daban za su halarta

Daga Jameel Lawan Yakasai

Za’a yi gagarumin taro na baje-kolin bajinta kan na’ura mai ƙwaƙwalwa a jihar Kano.

Taron, mai taken ‘Kano Digital Innovation Network'(KDIN), na 2025, shi ne karo na biyu da za a gudanar a jihar.

Shugaban shirya taron, Abdulsalam Hamza Maiturare, ya ce za a gudanar da taron daga ranar 22 zuwa 26 na watan Satumba, inda ya ce zai kasance mafi girma da muhimmanci a Arewacin Najeriya.

Maiturare ya bayyana cewa taron zai karfafa matsayin Kano a matsayin cibiyar kirkire-kirkire ta zamani a Arewa da yankin Sahel.

A cewar sa, bayan nasarorin taron ‘Digital Kano’ na farko da aka yi a bara, wanda ya jawo fiye da mahalarta 2,000 daga ko’ina a Najeriya da na duniya, wannan karo ana sa ran samun mahalarta sama da 5,000 ciki har da baki daga kasashen Afirka ta Kudu, Kanada, Amurka, Kenya da Zimbabwe.

KU KUMA KARANTA: Nan da shekarar 2030 rabin ayyuka za su koma kan na’urorin zamani – Masana

Taken taron na bana shi ne “Dorewar Tattalin Arziki: Magance Hada Hadar Kudi, Tsaron Abinci, Kalubalen Birane da Tattalin Arzikin Kore a Najeriya.”

Taron zai haɗa jama’a daban-daban kamar masu sha’awar kirkire-kirkire, masana fasahar sadarwa, ƴan kasuwa, hukumomin gwamnati da matasa. Maiturare ya ce shirin zai kunshi jawaban manyan baki, tattaunawa kan manufofi, nuna sabbin fasahohi, damar haɗin gwiwa a hanyoyin cigaba tsakanin jama’a da masu zaman kansu da na kasashen waje.

Ya shawarci wadanda ke sha’awar halarta su ziyarci gidan yanar gizon Kano Digital Innovation Network (KDIN) a www.digitalkano.ng don yin rijista da samun karin bayani.

Leave a Reply