Za a gurfanar da mutanen da ake zargi da rajin kafa ƙasar Yarbawa a kotu – Ƴan sanda

Rundunar ƴan sandan jihar Oyo da ke kudancin Najeriya ta ce nan gaba kaɗan za ta gurfanar da mutanen da ta kama bisa zargin fafutukar kafa ƙasar Yarbawa a gaban kotu.

A ranar Asabar da ta wuce ne, ƴan sanda suka kama ƴan kungiyar bayan mamayar da suka yi wa Ofishin gwamnar jihar Oyo da kuma majalisar dokokin jihar suna sanye da kakin soji kuma riƙe makamai daban-daban da kuma tutar ƙasar da suke son kafawa.

Kazalika rahotanni sun ce mutanen sun yi yunƙurin kutsa kai cikin ofishin gwamnan jihar, amma jami’an tsaro su fatattake su tare da kama da dama daga cikinsu.

Ana zargin matar hamshakin ɗan kasuwa kuma fitaccen ɗan siyasa, marigayi Cif Moshood Abiola, mai suna Dupe Onitiri- Abiola da ɗaukar nauyin masu fafutukar bayan wani bidiyo da ta wallafa wanda ya karaɗe shafukan intanet, tana mai iƙirarin ɓallewa daga Najeriya da kuma kafa shugabancin ƙasa ga al’ummar Yarbawa.

KU KUMA KARANTA: Rashin tsaro: Gwamnoni 16 na goyon bayan kafa ‘yan sandan jihohi

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Oyo, Hamzat Adebola, ya bayyana lamarin a matsayin laifi da rashin kishi da cin amanar ƙasa da kuma ayyukan ta’addanci a yayin da yake gabatar da mutanen da ake zargi a gaban ‘yan jarida, yana mai cewa ”za a hukunta su bisa tanadin doka.”

“Da farko ƴan sanda sun gargaɗi masu fafutukar da su watse amma sai suka yi kunnen-ƙashi daga nan gangaminsu ya juya zuwa rikici sai suka buɗe wuta kan ‘yan sanda da kuma tawagar jami’an sa-kai na Amotekun da ke wurin,” a cewar kwamishinan.

”An ƙwato bindigogi masu sarrafa kansu guda biyar da wasu tarin makamai da kayan sojoji guda 72 da harsashai 405 da dai sauransu,” in ji Kwamishinan ƴan sandan.

Haka kuma jaridun Najeriya sun ruwaito cewa ƴan sandan jihar Oyo na neman Onitiri-Abiola ruwa-a-jallo, sai dai a yayin jawabin Kwamishinan bai ambaci sunanta ba amma mai bai wa Gwamnan Jihar Oyo shawara kan harkokin tsaro Mista Fatai Owoseni ya ce ana sane da cewa ita ce take jagorantar ƙungiyar ta masu rajin kafa ƙasar Yarbawa daga Najeriya.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Oyo ya ce rundunar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen tabbatar da haɗin kan Najeriya.

“Ina so na yi amfani da wannan dama wajen tunatar da masu aikata laifuka cewa jihar Oyo jiha mai karɓar baki da kuma haziƙan mutane waɗanda ke alfahari da kansu a fannin ƙirƙire-ƙirƙire, da kuma aiki tuƙuru da wadata,” in ji shi.

Wasu daga cikin waɗanda aka kama sun shaida wa manema labarai cewa ba su yi nadamar mamayar da suka yi wa Ofishin gwamnatin jihar ba.

Sun ce sun bi matakai da suka kamata kuma ba su ci amanar ƙasa ba. “Ba mu yi nadama ba, mun bi tsarin da ya kamata mu bi,” kamar yadda suka shaida wa manena labarai.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *