Za a fuskanci zafin rana mai tsanani a Kano da wasu jihohin Arewa 17 — NiMet
Daga Shafa’atu Dauda Kano
Hukumar Kula da Yanayi ta Ƙasa (NiMet) ta fitar da gargaɗi kan yiwuwar tsananin zafin rana da ke barazanar jefa lafiyar jama’a cikin haɗari a wasu sassa na Arewacin Najeriya.
A cikin sanarwar da hukumar ta fitar ranar Juma’a, an bayyana cewa jihohin da za su fi fuskantar wannan zafi sun haɗa da: Gombe, Borno, Adamawa, Taraba, Yobe, Bauchi, Jigawa, Kano, Katsina, Kaduna, Zamfara, Sokoto, Kebbi, Neja, Kogi, Nasarawa, Benue da Babban Birnin Tarayya (FCT).
Sanarwar, wacce Manajan Yanayi na Jihar Gombe, Malam Gayus Musa, ya miƙa wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a ranar Asabar, ta nuna cewa daga ranar 12 ga Afrilu, ana sa ran yanayin zafi zai kai har digiri 40 na ma’aunin Celsius.
Bayan kwanaki uku da aka samu ruwan sama a wasu yankuna, an hango hauhawar yanayin zafi tare da ƙarancin hadari a sararin samaniya. Wannan zai iya haifar da rashin jin daɗi da kuma barazana ga lafiyar jama’a,” in ji sanarwar.
Malam Gayus Musa ya ja hankalin jama’a da su ɗauki matakan kariya domin kauce wa illolin wannan zafi. Ya ce yana da muhimmanci mutane su guji yawan fita da rana, su zauna a wuraren da ke da iska, da kuma shan ruwa da yawa.
KU KUMA KARANTA:Hukumar NiMet ta yi hasashen ruwan sama da tsawa na kwanaki 3
“Ina shawartar mutane su zauna a ɗakuna masu iska, su sanya tufafi masu launin sanyi da sassauci, su guji fita da rana tsakanin ƙarfe 12 na rana zuwa 3 na yamma, da amfani da duk wani abu da zai iya kare jiki daga rana,” in ji Musa.
Haka kuma, ya jaddada muhimmancin kula da ƙungiyoyi masu rauni kamar yara ƙanana da tsofaffi waɗanda zafin rana ke fi shafa. Ya bukaci masu ruwa da tsaki da su ƙara wayar da kai kan hadurran zafi da matakan kariya
Hasashen na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya ke shiga yanayin damina, lokacin da ake yawan fuskantar sauyin yanayi. NiMet ta bayyana cewa irin waɗannan sauye-sauye kan shafi lafiyar jama’a, musamman a yankunan Arewacin ƙasar.
Hukumar ta kuma buƙaci haɗin gwiwa da goyon bayan jama’a da hukumomi wajen faɗakar da al’umma da ɗaukar matakan kariya domin rage tasirin zafin rana da kuma kare rayukan mutane.