Zaɓen 2027: PDP ta ware kujerar takarar shugaban ƙasa a yankin Kudancin Najeriya 

0
338
Zaɓen 2027: PDP ta ware kujerar takarar shugaban ƙasa a yankin Kudancin Najeriya 

Zaɓen 2027: PDP ta ware kujerar takarar shugaban ƙasa a yankin Kudancin Najeriya

Daga Jameel Lawan Yakasai

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta ware kujerar ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓe mai zuwa na Shekarar 2027 ga yankin kudancin ƙasar nan.

Jam’iyyar ta tabbatar da haka ne a babban taron majalisar zartarwarta karo na 102 da ta gudanar a Litinin din data gabata a babban Birnin Tarayya Abuja.

A cikin sanarwar da Sakataren Yaɗa Labaran PDP na Ƙasa, Hon. Debo Ologunagba, ya fitar bayan taron na NEC, PDP ta bayyana gamsuwa da shirin da aka kammala domin babban taron ta na ƙasa (National Elective Convention) da za a yi a Ibadan, Jihar Oyo daga ranar Asabar 15 zuwa Lahadi 16 ga Nuwamba, 2025.

KU KUMA KARANTA: Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya fice daga PDP

Babban Ƙuduri da Matakan da PDP ta Dauka:

1. Shirin Babban Taro: An yaba da jajircewar PDP Governors’ Forum, BoT, NWC da sauran jiga-jigan jam’iyyar wajen shirya taron a Ibadan.

2. Rarraba Muƙamai: An amince cewa duk muƙaman da suke Arewa za su ci gaba da kasancewa a Arewa, haka nan na Kudu su ci gaba da kasancewa a Kudu.

– An tabbatar da cewa kujerar shugaban jam’iyya na ƙasa za ta ci gaba da kasancewa a Arewa.

– An yanke hukunci cewa ’yan takarar shugabancin ƙasa na 2027 za su fito daga Kudu.

– Kowane shiyya ta yi micro-zoning na cikin gida don rabon muƙamai.

3. Sauyin Tsarin Mulki: An umarci kwamiti mai duba kundin tsarin mulki ya rarraba kwafin da aka gyara zuwa rassan jam’iyya domin karin shawarwari.

4. Sabon Shugaban Jam’iyya: NEC ta tabbatar da nadin Amb. Iliya Umar Damagum a matsayin shugaban jam’iyya na dindindin har zuwa taron Ibadan na watan Nuwamba.

KU KUMA KARANTA: Zan yi haɗaka da sabuwar jam’iyyar ADC don a kayar da Tinubu, amma ba zan fice daga jam’iyar PDP ba – Sule Lamiɗo

5. Suka ga APC: PDP ta la’anci APC bisa “cusa hannun gwamnati cikin zaɓe”, tare da amfani da tsoro, karfin soja da tilas wajen murƙushe zabe musamman a jihohin Kaduna, Taraba da Zamfara.

6. Barazanar Mulkin Jam’iyya Ɗaya: PDP ta ce irin wannan salon da APC ke bi na nuni da cewa tana ƙoƙarin maida Najeriya ta zama jam’iyya ɗaya tilo, wanda ke barazana ga dimokuradiyya da zaman ƙasar baki ɗaya.

7. Alƙawari ga ’Yan Najeriya: PDP ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da kare dimokuradiyya da muradun al’umma tare da ƙarfafa jam’iyya domin komawa mulki a 2027.

8. Taron Gaba: An saka ranar 15 ga Oktoba, 2025 a matsayin ranar taron NEC na gaba (103).

Haka kuma jam’iyyar ta tabbatar da Umar Iliya Damagum a matsayin shugabanta na ƙasa a hukumance.

A baya-bayan nan dai an ga yadda wasu ƴan jam’iyyar suka zafafa kiraye-kiraye ga tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan ya yiwa jam’iyyar takara a zaɓen 2027.

Abun jira a gani dai shine, shin ko Jonathan din zata iya tsayar ko kuma wani daga yankin kudun, wanda yake da karfin hada kafa da Shugaba mai ci da ya fito daga babbar jam’iyyar hamayya ta APC, kuma wanda jam’iyyar take gannin shine zata kara sanyawa gaba domin karashen Zango mulkinsa 2, wato Ahmad Bola Tinubu.

Leave a Reply