Zaɓen Amurka: Trump da Harris na buƙatar zage damtse don samun nasara a jihar Georgia

0
31
Zaɓen Amurka: Trump da Harris na buƙatar zage damtse don samun nasara a jihar Georgia

Zaɓen Amurka: Trump da Harris na buƙatar zage damtse don samun nasara a jihar Georgia

Jihar Georgia ta riƙa nuna alamun sake zaɓen tsohon shugaban Amurka Donald Trump a farko-farkon yaƙin neman zaɓen shugabancin Amurka a shekarar 2024, lokacin da shugaba Joe Biden ke bisa takarar, to amma mataimakiyar shugaban ƙasa Kamala Harris ta maida wasa sabo zuwa ga jam’iyar Democrat.

A yanzu dai ana ɗaukar Georgia a matsayin daya daga cikin manyan jihohin raba gaddama a sakamakon zaben, wanda duk da haka ake ganin Harris nada saura zage damtse.

Duk da dai cewa, Biden ya lashe Georgia a zaben shekarar 2020, da ya kai ga karshen nasarar da jam’iyar Republican ta saba yi a jihar tsawon shekaru 30, yayi nasarar ne da dan kankanin rinjayen kuri’u.

KU KUMA KARANTA:Joe Biden ya janye daga takarar shugaban Amurka

Idan har zatayi nasara, to wajibi ne Harris ta samu gagrumar nasarar kuri’un bakar fatar wadanda bisa al’ada suka saba zaben jam’iyar Democrat. To amma shima Trump ya rika zawarcin wadannan masu kada kuri’ar, da sakamakon ra’ayoyin jama’a da aka rika tattarawa ya nuna ya rika samu nasara akai.

A zaben da zai kasance na kud da kud, al’amurra da dama na iya tasiri a sikelin kowane daga cikin yan takarar, da ya hada da fannin tattalin arziki, shigi da fici, yancin zubar da ciki da dokar mallakar bindiga, da uwa uba, tabbatar da dorewar Democradiyya.

Jihar Georgia wuri ne dake kan takaddama inda ake zargin Trump da makarraban shi da hadin bakin neman sauya kayen da ya sha a zaben shekarar 2020.

Leave a Reply