Zaɓaɓɓen ɗan majalisar wakilai ya ba da gudumawar shanu 59 a mazaɓarsa a Zamfara

5
704

A ranar Talata ne zaɓaɓɓen ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Maru da Bunguɗu a jihar Zamfara, Abdulmalik Zubairu ya bayar da gudunmuwar shanu 59 ga al’ummar mazabar sa domin gudanar da bukukuwan Sallah ƙarama

Da yake jawabi a lokacin rabon dabbobin a Bunguɗu, zaɓaɓɓen ɗan majalisar ya bayyana cewa hakan na daga cikin shirye-shiryen jin daɗinsa ga jama’a domin gudanar da Sallah.

Malam Zubairu, wanda tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar Bunguɗu, Basharu Bello-Auki ya wakilta, ya ce waɗanda suka ci gajiyar tallafin sun haɗa da membobin zartaswa na jam’iyyar APC daga mazaɓu 21 na ƙananan hukumomin Bunguɗu da Maru.

KU KUMA KARANTA: Yadda jam’iyyar PDP ta kwace kujerar gwamna a Zamfara

Bello-Auki kuma shi ne Shugaban kwamitin rabon kayayyakin. Wasu kuma, ya ce, marayu ne, zawarawa, ‘yan gudun hijira, matasa da ƙungiyoyin mata. “Wannan baya ga kayan abinci da muka raba a farkon watan Ramadan.

Zaɓaɓɓen ɗan majalisar ya buƙaci kwamitin da ya tabbatar da adalci yayin raba dabbobin.

Da yake mayar da martani a madadin waɗanda suka ci gajiyar tallafin, shugaban gidauniyar Zannah Foundation reshen jam’iyyar APC reshen Maru, Nasiru Sani ya yabawa zaɓaɓɓen ɗan majalisar bisa wannan karamcin.

Sani ya ce kwamitin zai tabbatar da yadda za a raba dabbobin ga waɗanda suka ci gajiyar.

5 COMMENTS

Leave a Reply