Gwamnatin Yobe ta haramta bukukuwan ‘Marker Day’ a dukkan makarantun Sakandire, saboda lalata tarbiyya

0
284
Yobe ta haramta bukukuwan ‘Marker Day’ a dukkan makarantun Sakandire, saboda lalata tarbiyya
Gwamnan Yobe, Dakta Mai Mala Buni

Gwamnatin Yobe ta haramta bukukuwan ‘Marker Day’ a dukkan makarantun Sakandire, saboda lalata tarbiyya

Ma’aikatar Ilimi ɓangaren babbar Sakandire ta jihar Yobe ta sanar da dakatar da gudanar da bukukuwan ‘Marker Day’ a makarantun gwamnati da masu zaman kansu a faɗin jihar nan take.

A cikin wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar, gwamnatin ta nuna matuƙar damuwarta kan yadda irin waɗannan bukukuwa ke kara ta’azzara, waɗanda ke da alaƙa da hargitsi, da ta da hankulan jama’a, da yin abubuwan da ke zubar da kimar al’umma da lalata tarbiyya.

A cewar ma’aikatar, waɗannan al’amuran sun kauce wa ayyukan makaranta da aka amince da su kuma a yanzu suna yin barazana ga horo da tsaro a cikin yanayin koyarwa.

KU KUMA KARANTA: Gwamnan Yobe ya biya bashin Naira biliyan 39, ya jaddada tsare-tsaren tattalin arziƙi

Sanarwar ta kuma ƙara da cewa, matakin haramtawar na ranar kammala Sakandire da ɗalibai ɗin suke yi, sai ya zama sun mayar da ranar ta kasance ranar gurɓacewar tarbiyya, da ɗabi’un da suka saɓa wa kimar ilimi da zama ɗan ƙasa.

Ma’aikatar ta yi gargadin “An umurci dukkan shugabannin makarantun da su tabbatar da bin wannan umarnin.” “Duk makarantar da aka samu tana shiryawa ko kuma jure irin waɗannan abubuwan za ta fuskanci hukuncin ladabtarwa da ya dace.”

Gwamnati ta jaddada ƙudirinta na kiyaye tsarin ilimi mai inganci a faɗin jihar.

Leave a Reply