No menu items!

Sample Page Title

Date:

Ana zargin wani mutum mai suna Atumu Treasure wanda ake wa laƙabi da Oluwa Benz Richer, da dukan wata budurwarsa mai suna Peace saboda ta ƙi aurensa.

An bayyana cewa, masoyan sun rabu ne na watanni shida da suka gabata a garin Irri da ke ƙaramar hukumar Isoko ta kudu a jihar Delta.

A cewar wani mai fafutukar kare haƙƙin ɗan Adam, Israel Joe, wanda ya bayyana labarin a shafinsa na Instagram, mutumin ya shiga gidan Peace, inda ya kulle ƙofa, ya fara dukanta, da shaƙe ta saboda ta ƙi aurensa.

Joe ya ce, maƙwabta ne suka ji kukan matar, suka cece ta daga tsohon masoyin nata kuma suka kama shi.

KU KUMA KARANTA:Budurwa tayima saurayin ta duka bayan ta kamashi da mamanta, a Abuja

Ɗan gwagwarmayar ya yi kira ga kwamishinan ‘yan sandan jihar Delta, Ari Mohammed Ali, domin tabbatar da an gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu, yana mai cewa ana tattauna bada belin shi a ofishin ‘yan sanda na Oleh.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

2 COMMENTS

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...