‘Yansanda a Yobe sun kama wani matashi bisa zargin kisan kai
Rundunar ’yansandan jihar Yobe ta kama wani ɗan shekaru 24 bisa zargin kashe Lawan Adamu, mai shekaru 28 a Unguwar Nayi-Nawa cikin garin Damaturu, babban birnin jihar.
Kakakin rundunar, DSP Dungus Abdulkarim ya ce, “A ranar 15 ga Satumba, ‘A’ Division Damaturu ta samu ƙiran waya kan gawar da aka tsinta.
“Nan take jami’anta suka isa wurin suka gano wanda abin ya shafa da yanka a maƙogwaro da raunuka masu yawa; kuma sun kuma gano wuƙa mai ɗauke da jini a wurin a jefe.
“An kai gawar zuwa babban asibitin Damaturu, inda wani likita ya tabbatar da rasuwar sa sai aka ajiye gawar a ɗakin ajiyar gawa na asibiti.”
KU KUMA KARANTA: Yan sanda sun kama wani da ya caka wa ’yar shekara 8 almakashi a gabanta
A cewarsa, “wanda ake zargi da aikata wannan aika-aika a kan hanyar unguwar Nayi-Nawa ya kama marigayin da kokawa sanadiyar takaddama tsakaninsu, daga bisani ya daba masa wuƙa a wuyansa ya jefar da shi nan ta ke a mace.
“Kwamishinan ’yan sandan jihar Yobe, Garba Ahmed, ya ba da umurni a faɗaɗa binciken domin gano musabbabin faruwar lamarin.
“Ya kuma tabbatar wa da jama’a cewa za a gaggauta gudanar da bincike, domin kuwa tabbas za a yi adalci.