‘Yan Yahoo-Yahoo ne suka janyo aka saka wa Najeriya tsauraran matakai akan yin biza – EFCC
Hukumar EFCC ta ce yawaitar damfarar yanar gizo na daga cikin dalilan da kasashen waje ke tsaurara dokokin Biza ga ‘yan Najeriya marasa laifi.
Shugaban hukumar, Ola Olukoyede, wanda CSE Coker Oyegunle ya wakilta a wani taro a Fatakwal, ya ce damfara tana lalata makomar matasa, tana jawo wa kasar asarar biliyoyin naira da kuma bata sunan Najeriya a duniya.
Ya gargadi matasa da su daina bata karfinsu a kan “yahoo-yahoo” su mayar da hankali kan kirkire-kirkire, noma, kasuwanci da masana’antar kere-kere.
KU KUMA KARANTA: ‘Yan Yahoo na kunyata Najeriya a idon duniya — shugaban EFCC
EFCC ta ce damfara ba nasara bace, illa ce da ke kaisu ga asarar ‘yanci, mutunci da makoma, tare da jawo musu tsauraran sharuddan Biza a kasashen waje.
Hukumar ta kuma ce tana kara kaimi wajen yakar damfarar yanar gizo a fadin kasar, inda aka cafke masu yawa a Lagos a watan Agusta.









