Daga Idris Umar, Zaria
A ranar Alhamis ne mutanen garin Marke dake ƙaramar hukumar Makarfi ta jihar Kaduna suka wayi garin da tashin hankali mai girma.
Neptune Prime Hausa ta ziyarci wannan garin don samun bayanai akan abin da ya faru.
Ganau ya tabbatar da cewa, wasu da ba’asan su wa suka shigo garin na Marke da misalin karfe 1 na dare suka ɓalle kofar gidan sarki suka kamashi suka ɗaure shi kamar dabba suka yankashi kamar rago daga bisani suka cinnawa gidansa wuta.
Bayan sun kora kowa a cikin gidan maza da mata.
Binciken da Neptune Prime Hausa tayi ta tabbatar da cewa basu ɗauki komi a cikin gidan ba, kuma basu tafi da kowa ba, sarkin kawai suka kashe suka tafi.
Mun ta zanta da shugan ƙaramar hukumar ta Makarfi game da lamarin ya faru wato Honorabul Kabiru Mu’azu,Miyare shima ya nuna damuwarsa matuƙa akan lamarin ƙarshe yace, suna nan suna addu’ar Allah ya tona asirin duk wanɗanda sukayi wannan aika-aikar kuma ya tabbatar da cewa suna daukar matakin daya dace akan lamarin.
KU KUMA KARANTA: Ƴan bindiga sun yi garkuwa da ɗalibai da dama a jihar Delta
Shima Ɗan majalisar dokoki na yankin, Honorabul Isyaku Ibrahim, ya shaida lamarin kuma ya tabbatarwa kafar watsa labarai na Neptune Prime Hausa cewa, sun ga tashin hankali sosai amma suna roƙon Allah ya tona asirin duk masu yin irin wannan mummunan aikin a ƙasa baƙi ɗaya karshe yace, a hukumance suna ƙokarin daukar mataki amma ya roƙi al’umma da su dage da addu’a samun zaman lafiya a ƙasa baƙi ɗaya.
Bincike ta tabbatar da cewa sarkin ya bar duniya yanada shekaru 30, kuma yana da mace 1 yara 2.
Mun yi tayi ƙoƙarin jin ta bakin ƙaƙakin rundunar yan’sanda na jihar Kaduna ta wayar salula amma hakan ya ci tura.
Bisa haka ne shugaban ƙaramar hukumar ya tabbatar da faruwar lamarin kuma ya jajantawa dangi da abokan arziki.









