Harin ‘yan bindiga ya sabbaba kisan mutane 10 da yin garkuwa da masu unguwanni 2 a Kaduna

0
102

‘Yan bindiga sun hallaka aƙalla ‘yan sintiri 8 da wasu mutane 2 a ƙauyukan Kakangi da Unguwan Matinja dake ƙaramar hukumar Birnin Gwarin jihar Kaduna.

‘Yan bindigar sun kuma yi awon gaba da masu unguwannin Kakangi da Kisiya a gundumar ta Kakangi.

Wani mazaunin yankin mai suna, idris khalid, wanda ya tabbatarwa manema labarai aukuwar lamarin yace, wasu mutane ne ɗauke da muggan makamai suka mamaye ƙauyukan a jiya Alhamis suna harbin kan mai uwa da wabi.

KU KUMA KARANTA:Tilas mu ɗauki masu garkuwa da mutane a matsayin ‘yan ta’adda – Bola Tinubu

Idris Khalid ya ci gaba da cewar, ‘yan sintirin sun yi ba-ta-kashi tsakaninsu da ‘yan bindigar, inda suka hallaka da dama daga cikinsu sai dai ba su iya ceto masu unguwannin da sauran jama’ar ba.

A cewarsa, “a bisa al’ada, duk sa’ilin da aka yi garkuwa da mutane, ‘yan sintiri kan bi sawun ‘yan ta’addar da nufin ceto waɗanda aka sacen”.

Ya kuma ƙara da cewar, “a wannan karon an yi rashin sa’a a aikin ceton, inda aka rasa rayukan 8 daga cikin zaratan jami’an sintirin da suka jima suna sadaukar da rayukansu wajen tabbatar da tsaron al’umma”.

A cewar Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan, ana ci gaba da gudanar da bincike akan lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here