‘Yan ta’adda sun yi barazanar dasa bom a kasuwar waya ta Kano 

0
196
'Yan ta'adda sun yi barazanar dasa bom a kasuwar waya ta Kano 

‘Yan ta’adda sun yi barazanar dasa bom a kasuwar waya ta Kano

Daga Shafaatu Dauda Kano

Ana zaman fargaba a Kasuwar Wayoyi dake Bata a jihar Kano, bayan da wasu da ba a san ko su wanene ba suka aike da saƙon barazanar tayar da bama-bamai a cikin kasuwar.

Shugaban kasuwar, Alhaji Mahrazu Usman Lawan, ya tabbatar da faruwar lamarin ga Manema labarai, inda ya bayyana cewa an fara aika masa da saƙon barazana tun daga yammacin ranar Lahadi.

KU KUMA KARANTA: Sarkin Kano Sanusi, ya bawa ‘yan kasuwar waya da iftila’in gobara ta shafa tallafin Naira miliyan 10

A cewarsa, masu barazanar sun nemi a basu naira miliyan goma domin kaucewa tada bama-bamai a kasuwar, tare da bayyana cewa sun rigaya sun ɗaura abubuwan fashewa a shaguna guda bakwai.

Nan da nan shugaban kasuwar ya sanar da hukumomin tsaro, inda aka soma bincike tare da ƙara sa ido kan harkokin a’lumma a kasuwar.

Daga baya kuma, masu barazanar suka ci gaba da kiran waya kai tsaye.Alhaji Mahrazu ya ce jami’an tsaro sun gudanar da bincike sosai a kasuwar, amma ba su samu wata na’urar fashewa ba.

Hakan ne ya sa aka buɗe kasuwar a ranar Litinin har zuwa ƙarfe 5 na yamma.

Sai dai ya ƙara da cewa har zuwa tsakiyar ranar Litinin, masu barazanar na ci gaba da aika saƙonni, inda suka ce a jira dare domin ganin abin da zai faru.

Leave a Reply