Sarkin Kano Sanusi, ya bawa ‘yan kasuwar waya da iftila’in gobara ta shafa tallafin Naira miliyan 10

0
128
Sarkin Kano Sanusi, ya bawa 'yan kasuwar waya da iftila'in gobara ta shafa tallafin Naira miliyan 10

Sarkin Kano Sanusi, ya bawa ‘yan kasuwar waya da iftila’in gobara ta shafa tallafin Naira miliyan 10

Daga Jameel Lawan Yakasai

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ll ya baiwa ƴan kasuwar waya ta Farm Centre tallafin Naira miliyan 10 sakamakon gobara da ta ƙone shaguna da rumfuna 47 a kasuwar a jiya Juma’a.

Sarkin ya bayyana wannan tallafi ne yayin da ya kai ziyarar nake ga kasuwar, inda ya shawarci su buɗe asusun tallafi don farfaɗo da sashen da ya kone a kasuwar, lamarin da ya haifar da nasara dukiya ta miliyoyin Naira.

KU KUMA KARANTA: Gobara ta ƙone shaguna 47 a kasuwar waya ta a Kano

A cewar Sarki Sanusi, ya bada tallafin kuma ya na kira ga waɗanda abun ya shafa da su buɗe asusun tallafi su kuma aikewa duk wanda ya ke kasuwar.

Ya kara da cewa nan gaba kadan za a tara makudan kudade da za su isa a gyara kasuwar, su kuma yan kasuwa su rage asara.

Sarki Sanusi ya kuma yi addu’ar Allah Ya kiyaye faruwar gobarar nan gaba, inda ya yi wa wadanda lamarin ya shafa addu’ar Allah Ya kawo musu ɗauki.

Leave a Reply