No menu items!

Sample Page Title

Date:

‘Yan sanda a ƙasar Thailand sun kama wani magidanci bisa zargin shi da lakaɗa wa ‘yarsa tare da wasu ƙananan ‘ya’yansa dukan da ya yi sanadiyyar mutuwar su.

Haka nan kuma mutumin, mai suna Songsak Songsaeng ya kashe wasu ‘ya’yansa maza ƙanana guda biyu a lokacin da yake auren tsohuwar matarsa.

Waɗannan tuhume-tuhume sun biyo bayan gano gawar ‘yarsa mai shekara biyu binne cikin ɗakin girki.

Sai dai binciken da ‘yan sandan suka gudanar ya gano cewar mutumin yana da lalular ƙwaƙwalwa, ya kuma kashe yaran ne saboda ba ya son koke-kokensu.

An tuhumi matarsa da laifin mutuwar ‘yarsu mai shekaru biyu, yayin da tsohuwar matarsa ke fuskantar tuhumar mutuwar ‘ya’yanta maza biyu. Dukkan iyayen uku na tsare a hannun jami`an tsaro.

A farkon wannan wata maƙwabtan Mista Songsak suka sanar da jami`an tsaro a yankin Bang Ken cewar ya na dukan ‘ya’yansa mata, rahoton da ya sa ‘yan sanda suka ceto yaran daga gidan.

Gwajin ƙwayoyin halitta da jami`an tsaro suka gudanar ya tabbatar da Mista Songsak ya kashe wasu ‘ya’yansa maza biyu da ya haifa da matarsa ta uku waɗanda aka tono gawarsu shekaru goma da suka wuce, bayan mahaifiyarsu ta shaida wa ‘yan sanda yadda ya kashe jarirai huɗu.

‘Yan sandan sun tabbatar da ya binne sauran gwawarwakin ne a harabar wani tsohon gidan mai.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...