‘Yan sanda sun kama wanda ake zargi da kashe tsohon DPO a Ribas

Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Bayelsa sun kama ɗaya daga cikin waɗanda suka kashe SP Bako Angbashim, tsohon jami’in ‘yan sandan shiyya ta Ahoada, jihar Ribas.

A cikin wata sanarwa da aka saki a yau 18 ga watan Nuwamba, kakakin rundunar, CSP Buswat Asinim, ya ce wanda ake zargin, Onyekachi Ikowa’, 43, wanda shi ne na biyu a matsayin kwamandan TuBaba na ƙungiyar asiri ta Iceland, an kama shi ne a ranar 18 ga watan Nuwamba 2023, bisa ingantattun bayanan sirri da ke nuna cewa yana ɓoye a Yenagoa bayan ya shiga cikin kisan gillar da aka yi wa Marigayi SP Bako Angbashim, a cikin Satumba 2023.

A halin da ake ciki, kwamishinan ‘yan sandan jihar Bayelsa, CP Francis Iduh, ya umarci ‘yan sanda da su kamo duk wata tawagarsa da ke ɓoye a jihar Bayelsa, ya kuma jaddada cewa rundunar ta Bayelsa da ke karkashin sa ba za ta zama mafakar masu aikata laifuka ba.

KU KUMA KARANTA: An kama mutane shida da ake zargi da kisan DPO na Ribas

LIB ta ruwaito cewa wasu da ake zargin yan kungiyar asiri ne a ranar Juma’a, 8 ga watan Satumba, sun harbe SP Bako Angbashim. 

Marigayin shugaban ‘yan sandan da mutanensa sun yi artabu da wani fitaccen shugaban ƙungiyar asiri a yankin da ake kira ‘’Tubaba’’ inda aka ce harsashi ya kare wa ƴan sanda, ‘yan ƙungiyar asiri sun kama DPO ɗin da ya samu raunukan harbin bindiga a yayin musayar wuta.  

A cikin wani faifan bidiyo da ake kyautata zaton ’yan ƙungiyar asiri ne suka fitar, an ga gawar Mista Bako da aka yanke aka yi mata gunduwa-gunduwa, yayin da aka ji wata murya tana masa ba’a.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *