‘Yan sanda a Zamfara sun kama waɗanda ake zargi da kisan ɗan jarida a jihar

0
282

Wasu ’yan uwa biyu suna tsare a ofishin ‘yan sanda na Tudun Wada da ke garin Gusau a Jihar Zamfara, bisa zargin kashe wani ɗan jarida wakilin Muryar Najeriya, Hamisu Ɗanjibga.

Waɗanda ake zargin, Bilal Haruna da, Mansur Haruna, ‘ya’yan yayan marigayi Ɗanjibga ne, Malam Haruna.

Suna zaune ne a gidan marigayi Ɗanjibga da ke unguwar Samaru a birnin Gusau, kafin kisan.

Ɗanjigba, wanda aka bayyana ɓacewarsa a ranar Asabar, 16 ga watan Satumba, ya koka a lokuta da dama kan rashin ɗa’a na mutanen biyu, waɗanda ‘yan uwansa ne.

Bayan ya ɓace ne aka aika da saƙo ga iyalansa.  A saƙon ta wayar salula, wanda ya aika ya buƙaci Naira miliyan ɗaya a matsayin wani ɓangare kafin a bayyana kuɗin fansa na ƙarshe ranar Juma’a.

KU KUMA KARANTA: Kwana uku da ɓatan ɗan jarida a Zamfara, an samu gawarsa a rami

Abin baƙin ciki, an tsinci gawarsa a ranar Laraba, 20 ga Satumba, an jefar da shi a wani soakway a bayan gidansa.

An kama ‘yan uwansa dangane da kisan nasa, yayin da ake ci gaba da bincike kan lamarin.

Ɗanjibga ya yi aiki a gidajen yaɗa labarai da dama kamar, Jaridar Ayau, Kunnen Gari, Muryar Najeriya da FM Nigeria.

Ya rasu ya bar mata da ‘ya’ya da jikoki.

Leave a Reply