No menu items!

Sample Page Title

Date:

‘Yan Najeriya fiye da miliyan 6.2 sun kammala matakin farko na rajistar katin zaɓe ta yanar gizo – INEC

Fiye da ‘yan Najeriya miliyan 6.2 ne suka kammala rajistar su ta yanar gizo a shirin ci gaba da rajistar masu zaɓe a mako na shida na aikin, a cewar bayanan da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta fitar a ranar Litinin.

Ƙididdigar da aka wallafa a shafin X na hukumar da kuma shafinta na yanar gizo ta nuna cewa jimillar 6,232,673 ne suka yi rajista tsakanin 22 zuwa 28 ga Satumba, 2025.

KU KUMA KARANTA: Mutane 387,187 ne ba su karɓi katin zaɓen su ba, a Kano – INEC

Daga cikin wannan adadi, mata sun kai 3,250,338 (kashi 52.15%), yayin da maza suka kasance 2,982,335 (kashi 47.85%). Matasa masu shekaru tsakanin 18 zuwa 34 sun fi rinjaye da adadin 4,230,715. Dalibai sun taka muhimmiyar rawa da 1,565,824, yayin da masu bukata ta mussaman suka kai 137,865.

INEC ta kuma bayyana cewa a mako na biyar (22–26 ga Satumba, 2025), mutane 1,004,132 daga cikin ‘yan Najeriya ne suka kammala rajistarsu ta yanar gizo da ta ofis.

Cikin wannan adadi, 537,743 sun kammala rajistarsu ta yanar gizo, yayin da 466,389 suka kammala ta ofis.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...