‘Yan Najeriya 376 da suka maƙale a Sudan, sun isa Abuja

Daga Haruna Yusuf

A ranar Laraba ne rukunin farko da aka kwaso daga Sudan da yaƙi ya ɗaiɗaita zuwa Masar sun iso gida Najeriya.

Mutanen da aka kora su ne rukunin farko da suka isa kan iyakar Argeen a makon jiya Laraba 26 ga Afrilu don jigilar jiragen sama a Aswan Masar.

Kashi na farko na mutanen da aka kwaso sun samu tsaiko sakamakon ƙa’idojin da hukumomin Masar suka bayar domin a kai su Najeriya ta jirgin sama.

A cikin wani faifayin murya da aka aike wa ɗakin taron hukumar kula da harkokin ƙasashen waje na Najeriya a ranar Laraba, wani jami’in Najeriya ya bayyana dalilan da suka sa aka samu jinkirin jigilar ‘yan Najeriya da ya kamata su iso ƙasar a safiyar yau.

Jami’in ya bayyana cewa, “Jirage guda biyu, Air Peace da kuma NAF C130, ya kamata su yi jigilar fasinjoji 350. Abin takaici, ƙarin mutane 26 sun kutsa cikin bas ɗin. Ma’aikatan Masar na can. Sun ƙirga sun gano ‘yan Najeriya 376.

KU KUMA KARANTA: Masar ta buɗe iyaka ga ‘yan Najeriya da suka tsere daga Sudan

Sun ƙi amincewa da mutane 26 da su tsaya a filin jirgin sannan kuma sun ƙi yarda jami’an Najeriya su mayar da mutanen 26 zuwa kan iyaka.

“Yanzu, suna son kowa ya tafi. Haka kuma ba za su bari su koma kan iyaka ba. Zaɓin kawai shi ne a yi lodin jirgin sama. An tuntuɓi matuƙan jirgin kuma sun ce ba za su iya jigilar mutane da yawa ba kuma suna da kaya da yawa.”

Sai dai jirgin na Air Peace ya isa da ƙarfe 11:35 na safe tare da fasinjoji 278 yayin da NAF C130 ya zo da ƙarfe 11:55 na rana tare da fasinjoji 98. Shugabar hukumar ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa ta bayyana fatan za a kwashe waɗanda ba su iso ba cikin gaggawa.

Dabiri-Erewa ta ce, “Kowa ya yi murna da karɓar su. Muna fatan waɗanda ke can za su dawo da sauri. Muna sa ran cewa da shirye-shiryen da NEMA ta yi, za a samu ƙarin jirage domin ƙasar Masar ta yi wahala.

“Ga ‘yan Najeriya da suka maƙale a Port Sudan, suna ƙoƙarin samun tikitin ne saboda ya ma fi wahalar samun jiragen zuwa Port Sudan. Amma suna da jirgin sama.

Suna sarrafa shi, kuma da zarar sun samu tikiti, za su dawo gida. Idan sauran kamfanonin jiragen sama sun sami izinin sauka, za su yi sauri su je su kwashe ‘yan Najeriya da suka maƙale. Mun yi farin ciki cewa babu wanda ya rasa ransa. An ba mata da yara fifiko.”

Dabiri-Erewa ta bayyana cewa rukunin farko na waɗanda aka kwaso daga Sudan za su isa Najeriya a daren Laraba. Ta bayyana hakan ne a shafinta na Twitter a ranar Laraba.

Ta wallafa a shafinta na twitter cewa, “Daga karshe, jirgin NAF C-130H ya taso daga Aswan kuma ana sa ran zai isa filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe Abuja da ƙarfe 11:23 na dare. #Sudan. Muna addu’ar Allah Ya kiyaye.”


Comments

One response to “‘Yan Najeriya 376 da suka maƙale a Sudan, sun isa Abuja”

  1. […] KU KUMA KARANTA: ‘Yan Najeriya 376 da suka maƙale a Sudan, sun isa Abuja […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *