‘Yan majalisar wakilai sun kammala tsare-tsaren raba motocin alfarma, duk da wahalhalun da ƙasa ke ciki

0
249

Yayin da ‘yan Najeriya ke fafutukar tinkarar mawuyacin halin da tattalin arziƙin ƙasar ke ciki sakamakon cire tallafin man fetur, majalisar wakilai ta bayyana cewa ta kammala shirye-shiryen rabon motocin hukuma ga ‘yan majalisar wakilai ta 10.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, shugaban kwamitin majalisar kan harkokin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Akin Rotimi, ya ce hukumar na cikin shirin sayo da raba motocin ga mambobin.

Wani ɓangare na sanarwar ya ce: “Ba kawai ‘yan Majalisar ba, domin jami’an gwamnati da ba a zaɓa a ɓangaren zartarwa na gwamnati ba tun daga matakin Mataimakin Darakta zuwa sama, a mafi yawan lokuta, suna da motocin hukuma a ofisoshinsu.

Yana da mahimmanci a yi bayani.  Motocin da za a ware wa ofisoshin ‘yan Majalisa motoci ne da aka tanada don ayyukan sa ido wajen gudanar da ayyukansu a kwamitoci.  Ba motocin sirri ba ne da aka baiwa mambobi masu daraja.  

KU KUMA KARANTA: Zulum ya ba da gudumawar motoci 50, babura 300 ga sojojin Najeriya

A tsawon lokacin Majalisa ta 10 (2023 – 2027), motocin za su ci gaba da zama mallakin Majalisar Dokoki ta ƙasa.  

A ƙarshen wa’adin majalisa ta 10 a shekarar 2027, idan har yanzu tsarin tafiyar da kadarorin gwamnati na nan daram yadda yake a yanzu, ‘yan majalisar za su iya samun zaɓin biyan kuɗin motocin  a asusun gwamnati kafin su zama nasu, in ba haka ba, motocin za su ci gaba da zama mallakin Majalisar Dokoki ta Ƙasa”. Ya ce.

Leave a Reply