‘Yan kasuwar Singa dake Kano, sun kwana cikin kasuwar don fargabar rushe musu shaguna
Daga Jameel Lawan Yakasai
Wasu matasa a kasuwar Singa titin Ado Bayero Kofar Gidan Kwali suke zaman gadin rumfunansu kenan, sakamakon yadda wani mai hannu da shuni suka zargi ya yi barazanar sanya wata Hukuma ta rushe musu.
Yan kasuwar sun ce ba za su bari a rusa musu rayuwa ta haryar durkusar da kasuwancinsu ba, in da suka sha alwashin kwana a kasuwar domin kare runfunansu, daga wannan dare na Lahadi har sai Gwamnati ta yi musu masalaha.
KU KUMA KARANTA: An buɗe babbar kasuwar Singa a Kano bayan kammala aikin tsaftace magudanar ruwa
Daya daga cikin yan kasuwar Nura Haruna Gobirwa yace, sun mallaki rumfunan tun sama da shekaru 40, kuma suna da takardu, don haka ba wanda za su bari ya zo ya rushe musu rumfa.
A karshe sun yi fatan Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf mai adalci ya shiga lamarin, kar ya bari a cuce su.









