Wasu da ake zargin ’yan ta’addan Boko Haram ne sun kai hari kan ayarin motocin Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, inda suka kashe ɗan sanda ɗaya.
Rahotanni sun ce an kai harin ne a kan ayarin a hanyar Maiduguri zuwa Damaturu a ranar Asabar, sannan aka jikkata wasu ’yan sandan su biyu.
Gwamnan na kan hanyarsa ce ta komawa Damaturu bayan ya halarci taron yaye ɗalibai karo na 24 na Jami’ar Maiduguri da ke Jihar Borno.
KU KUMA KARANTA: Sojoji da DSS sun daƙile yunkurin Boko Haram na kai hari a Kano
A cewar wani ganau da ke cikin tawagar da ya nemi a sakaya sunansa, maharan sun buɗe wuta kan ayarin motocin daga ɓangarorin biyu na babbar hanyar, inda suka nufi direbobin motar.
Majiyar ta ce “Mun tsira da kyar a yau, an kai wa ayarin motocinmu hari ne a tsakanin garin Beneshiekh da Mainok mai tazarar ƙasa da kilomita 60 zuwa Damaturu bayan halartar taro karo na 24 na yaye ɗaliban Jami’ar Maiduguri.
“’Yan ta’addan sun buɗe wuta kan ayarin motocin daga ɓangarori biyu, inda suka kashe ɗan sanda guda nan take, yayin da wata majiyar ta ce ɗayan kuma ya mutu daga baya sakamakon zubar jini da yawa saboda raunukan harsasai.
“Amma gaskiya mun bar Maiduguri a makare, sai wajen misalin karfe 5:40 na yamma,” in ji shi.
Sai dai Gwamna Buni ba ya cikin ayarin motocin a lokacin da lamarin ya faru kasancewar ya tafi Abuja ne domin gudanar da wani aiki.
Wannan dai shi ne karon farko da aka kai wa ayarin motocin Gwamnan hari tun bayan ɓarkewar rikicin Boko Haram shekaru kusan 13 da suka gabata.
Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, babu cikakken bayani kan yawan waɗanda aka kashe ko aka jikkata wa su ’yan ta’addan.