‘Yan bindinga sun kashe mutum 1, sun sace mutum 2 a garin Kwanar Ɗangora da ke Kano

0
270
'Yan bindinga sun kashe mutum 1, sun sace mutum 2 a garin Kwanar Ɗangora da ke Kano

‘Yan bindinga sun kashe mutum 1, sun sace mutum 2 a garin Kwanar Ɗangora da ke Kano

Daga Jameel Lawan Yakasai

Wasu mutane ɗauke da makamai sun kashe mutum ɗaya sannan suka yi garkuwa da mata biyu a  Kwanar Ɗangora, ƙaramar hukumar Ƙiru, ta jihar Kano.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 12:30 na daren Juma’a, lokacin da maharan masu yawa suka kai hari gidan wani Alhaji Ibrahim da ke Kwanar Ɗangora.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga a Kano sun yi garkuwa da mata 3

Rahotanni sun ce maharan sun yi garkuwa da matan Alhaji Ibrahim guda biyu Safara’u Ibrahim da Attine Ibrahim.

Maharan sun kuma harbe wani matashi mai suna Abdul Usman, mai shekaru 27.

Zuwa yanzu babu wata sanarwa daga rundunar yansanda.

Leave a Reply