‘Yan bindiga a Kano sun yi garkuwa da mata 3
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Yan bindiga sun yi garkuwa da mata 3 a garin garin Biresawa na Ƙaramar Hukumar Tsanyawa a Kano
Dagacin garin Yanchibi wanda Biresawa ke ƙarƙashinsa Malam Muhammad Shamsuddeen ya tabbatarwa Jaridar Neptune Prime faruwar lamarin.
KU KUMA KARANTA:‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane a garin Zakirai da ke Kano
Ya ce, ƴan taʼadda ɗauke da bindigu sun shiga gidan wani attajiri a garin Mai suna Alh. Musa Kande cikin dare, inda suka yi awon gaba da matansa biyu da ƴarsa guda ɗaya.
Har zuwa wannan lokacin ba a samu kira daga ƴan bindigar ba.