’Yan bindiga sun tarwatsa ƙauyuka 10 a Kaduna

0
194

’Yan bindiga sun tarwatsa al’ummar ƙauyuka 10 da ke zaune a yankin Kidandan na ƙaramar hukumar Giwa ta Jihar Kaduna.

Giwa dai na ɗaya daga cikin ƙananan hukumomin da ke fama da matsalar rashin tsaro a yankin Arewa maso Yamma.

Wasu daga cikin mazauna garuruwan da ta’adar ’yan bindigan ta tilasta musu yin ƙaura, sun koma ne babban garin Kidan da sauran yankunan da ke makwabtaka masu aminci a ƙaramar hukumar.

Ƙauyukan da abin ya shafa sun haɗa da Tunburktu, Hayin Dabino, Mugaba, Nasarawan Hayin Doka, Dokan Yuna, Doka, da Hayin Teacher.

Kansilan unguwar Kidandan, Abdullahi Ismail, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya koka da cewa a cikin makonni uku da suka gabata sojoji suna gudanar da ayyuka a kewayen yankin amma har yanzu ‘yan bindigar na ci gaba da kawo wa al’ummar farmaki.

Wani shugaban al’ummar, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce mazauna ƙauyukan da suka rasa matsugunansu sun bar kayan abincinsu da gidajensu saboda barazanar da ‘yan fashin dajin ke yi rayuwarsa da dukiyoyinsu.

KU KUMA KARANTA: An hukunta korarren sufeton ɗan sanda da ke satar makamai yana sayar wa ƴan bindiga

Ya kuma bayyana cewa a ranar Talatar da ta gabata sojojin da ke sintiri a yankin sun kashe kusan shida daga cikin ‘yan bindigar.

Ya ƙara da cewa, duk da cewa mazauna yankin sun ji daɗin kashe ‘yan bindigar da sojojin suka yi, amma suna shakkun bayyana farin cikinsu a fili.

Ya bukaci gwamnati da ta jibge karin jami’an tsaro domin kare sauran ƙauyukan da ’yan bindigar ka iya kaiwa hari.

Sai dai an yi rashin sa’ar jin ta bakin ASP Mansir Hassan, jami’in hulɗa da al’umma na rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna wanda wakilinmu ya tuntuɓa a yayin tattara wannan rahoto.

Leave a Reply