Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wata yarinya ‘yar shekara bakwai a ƙauyen Yangoji da ke ƙaramar hukumar Kwali a babban birnin tarayya Abuja.
Suleiman Musa, wani mazaunin ƙauyen ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN), a Abuja cewa ‘yan bindigar sun mamaye al’ummar ne da sanyin safiyar Laraba.
Ya ce ‘yan bindigar sun mamaye ƙauyen suna harbin bindiga sama kafin su kutsa cikin wasu gidaje inda suka damƙe yarinyar ‘yar shekara bakwai.
A cewarsa, shiga tsakani da tawagar ‘yan sanda suka yi cikin gaggawa ya tilastawa ‘yan bindigar ficewa daga ƙauyen.
KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun kashe mutane 37, sun jikkata da dama a jihar Sakkwato
(NAN) ta tattaro cewa hedikwatar ‘yan sanda ta Kwali ta amsa ƙiran kai harin da misalin ƙarfe 5 na safiyar Laraba.
Wata majiya ta ce, ɗaukin gaggawar da jami’an ‘yan sanda da mafarauta da ‘yan banga ƙarƙashin jagorancin jami’in ‘yan sanda na yankin Kwali, DPO suka yi ne suka ceci al’umma daga ci gaba da cutar da ‘yan bindigar.
Ya ce ‘yan bindigar sun yi artabu da jami’an tsaro kafin su tsere da yarinyar da aka sace.
Majiyar ta bayyana cewa, a halin yanzu rundunar tsaro na ci gaba da tseguntawa yankin da nufin ƙubutar da yarinyar tare da kamo ‘yan bindigar.
Da aka tuntuɓi jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda, PPRO, a babban birnin tarayya, SP Josephine Adeh, ta ce za ta dawo ga wakilinmu da zarar ta samu cikakken bayani kan lamarin.
[…] KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun sace yarinya ‘yar shekara 7 a Abuja […]