‘Yan bindiga sun sace shugaban ƙaramar hukuma tare da jama’arsa

0
161

Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da shugaban ƙaramar hukumar Akwanga a jihar Nasarawa Safiyanu Isah.

An yi garkuwa da Isah ne a daren Litinin, 1 ga watan Janairu, 2024, a ƙauyen Ningo, dake kan titin Akwanga-Andaha.

Mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Kamal Dauda Rija, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar, ya ce an sace shi ne tare da wasu, ciki har da wani fitaccen mai bayar da agaji a ƙaramar hukumar, Adamu Umar, wanda aka fi sani da Macciɗo.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun kashe wasu mutane a Nijar

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Ramhan Nansel, da jami’an tsaro da suka haɗa da ‘yan sanda da sauran hukumomi, sun yi gaggawar fara farautar waɗanda suka yi garkuwa da su domin ganin an sako waɗanda aka sace.

Leave a Reply